Sashen Yamoussoukro
Sashen Yamoussoukro | |||||
---|---|---|---|---|---|
department of Ivory Coast (en) | |||||
Bayanai | |||||
Ƙasa | Ivory Coast | ||||
Babban birni | Yamoussoukro | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ivory Coast | ||||
District of Ivory Coast (en) | Yamoussoukro Autonomous District (en) |
Sashen Yamoussoukro sashi ne na kasar Ivory Coast. Akwai babban birnin siyasa na Ivory Coast a karkashin sashen wato Yamoussoukro, kuma yana ɗaya daga cikin sassan biyu a gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kanta.
Yawan jama'a da ƙananan hukumomi
[gyara sashe | gyara masomin]Dangane da ƙidayar shekara ta 2014, Sashen Yamoussoukro na da yawan jama'a akalla mutum 310,056. [1] An raba sashen zuwa kananan hukumomi biyu, Yamoussoukro da Kossou.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An kafa Sashen Yamoussoukro a shekara ta 1988 azaman yanki na matakin farko yayin da aka rarraba Sashen Bouaké.[2] A shekara ta 1997, an gabatar da yankuna a matsayin sabon yanki na matakin farko na Ivory Coast; sakamakon haka, an mayar da dukkan sassan zuwa sassa na biyu. An haɗa Sashen Yamoussoukro a karkashin Yankin Lacs.
A cikin shekara ta 1998, an raba Sashen Yamoussoukro don kafa Sashen Tiébissou. [2] An sake raba Sashen Yamoussoukro a shekara ta 2009 don ƙirƙirar Sashen Attiégouakro. [2]
A cikin shekara ta 2011, an gabatar da gundumomin a matsayin sabbin yankuna a mataki na farko na kasar Ivory Coast. Bugu da kari, an sake tsara yankuna kuma sun zama yanki na biyu kuma an mayar da dukkan sassan zuwa matakai na uku. A wannan lokacin, Sashen Yamoussoukro ya zama wani yanki na gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kansa, ɗaya daga cikin gundumomi biyu na ƙasar waɗanda ba su da yankuna.
Bayanan kula
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Côte d'Ivoire", geohive.com, accessed 24 February 2016.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "Regions of Côte d'Ivoire (Ivory Coast)", statoids.com, accessed 16 February 2016.