Jump to content

Shinkafa da wake da mai da yaji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Shinkafa da wake abinci ne na hausawa mutanen arewacin nigeria,babba da yaro kowa yana son abincin ba don komai ba sai don dadin shi a baki da kuma kayatar da ido da yake yi.[1] Wake da shinkafa bai tsaya a iya dadi ba,yana dauke da sinadarai masu karawa jiki lafiya da takaita hadarin kamuwa daga cutar ciwon zuciya,ciwon sukari da kansa. Haka nan yana taimakawa wurin daidata kibar jiki duk saboda sinadarin wake da ke cikin sa. Hakanan masana kiwon lafiya sunce duk wani abinci da aka hada shi da rukunin abinci mai kara kuzari(wake) yana karawa abinci lafiya sosai

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://cookpad.com/ng-ha/recipes/7750947-shinkafa-da-wake-da-mai-da-yaji-da-salak-da-tumatur