Shittu Alao

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shittu Alao
Chief of the Air Staff (en) Fassara

5 ga Augusta, 1967 - 15 Oktoba 1969
Rayuwa
Haihuwa 1937
ƙasa Najeriya
Mutuwa 15 Oktoba 1969
Sana'a

Shittu Alao (an haife shi a shekara ta 1937 – 15 ga Oktoba 1969) shi ne babban hafsan hafsoshin sojin saman Najeriya daga shekara ta 1967 zuwa 1969.[1] Kanar Shittu shi ne kwamandan rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) na huɗu, kuma jami’i na biyu ɗan asalin ƙasar da ya riƙe wannan muƙamin.

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya rasu ne a ranar 15 ga watan Oktoba, 1969, a wani hatsarin jirgin sama a Uzebba, kimanin mil 50 arewa maso yammacin Benin.[2]Yana da shekaru 32 kuma shi kaɗai ne a cikin jirgi a yayin hatsarin. Bayan kwana biyu, a Legas, an yi jana'izar shi a cikin girmamawa irin ta soja.

An sanar da Emmanuel E Ikwue a matsayin wanda zai maye gurbinsa a ranar 18 ga Disamba, 1969.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]