Sneh Gupta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sneh Gupta (an haife shi 12 Mayu 1957) ƴar wasan kwaikwayo ce kuma babbar darektar Sucheta Kriplani Shiksha Niketan (SKSN), makarantar zama don ɗalibai masu ƙalubale na jiki. An san ta da aikinta a gidan talabijin na Burtaniya da ke haska shirin Sale of Century da Angels, da kuma rawar da ta taka a matsayin Gimbiya Sushila a cikin fim ɗin The Far Pavilions. Ta kuma kafa kamfanin samar da kayayyaki.[1]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Gupta a Kenya ranar 12 ga Mayu 1957.[2] ta na ɗaya daga cikin yara biyar ga iyaye ƴan Indiya. Mahaifinta malami ne kuma ta halarci makarantar da yake koyarwa. [3]

Ta yi tafiye-tafiye tun tana ƙarama domin ta bi aikin koyarwa na mahaifinta. [1] Duk da haka, ba ta son yin aure kuma tana son ƴancin kanta, ta bar gida tana da shekara 17 kuma ta shafe shekara guda tana karatu a Jamus kafin ta tafi Ingila. [3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Donnell, Alison (2002). Companion to Contemporary Black British Culture. Routledge. p. 132. ISBN 9780415262002 – via Google Books.
  2. "Sneh Gupta". British Film Institute. Archived from the original on 26 March 2019. Retrieved 14 April 2021.
  3. 3.0 3.1 Empty citation (help)

Hanyoyin Hadi na waje[gyara sashe | gyara masomin]