Sufanci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sufanci kalmace wacce take da mahanga da dama game da inda tasamo asali, domin malamai da yawa sunyi bayani game da asalin kalmar wasu suna ganin cewa ta samo asali ne daga Yaren girka inda take nufin (sofiya) ma'ana hikima, domin duk inda tasamo sufi zaka samu yanada hikima. To hakan yana nuna cewa sufanciwata hanya ce ta tunani akan hikimomi Ubangiji da halittun Allah (s.w).[1][2]

Sufaye

Haƙiƙanin sufanci[gyara sashe | gyara masomin]

Amma wasu suna ganin ban dauko Sufanci ne daga Zuhudu (gudun Duniya), sai Sufayen suka yi sakaci, suka halasta rawa da waka da jin, sai masu son Lahira cikin amawa (mutane gama gari) mutane suka bi su saboda gudun Duniya, sai kuma ‘Yan Duniya suka bi su saboda son holewa da cashewa.

Kasuwar addini wurin sufaye[gyara sashe | gyara masomin]

Sufaye suna kasa Addini zuwa:

Abin da suka dauko daga Kungiyoyin Badiniyya. Abin nufi da Shari’a a wajen Sufaye shi ne abin da dukkan mutane suka yi tarayya a cikinsa na lamarin Addini, wanda ake dauko shi daga Alkur’ani da Hadisi da Ijma’i, kamar Tsarki, Sallah, Azumi da sauransu. Don haka ma’abota Shari’a su ne ‘Yan Zahiri, wadanda suka kasa su gida biyu: 1- Amawa masu yin Sallah da Azumi. 2- Malaman Shari’a, wadanda ba su san hakika da badini ba, kawai su zahirin Nassoshi suka sani da kuma hukunce-hukuncen Shari’a na Tsarki da Sallah da Azumi.

Su waye'yan haƙiƙa[gyara sashe | gyara masomin]

‘Yan Hakika sune Sufaye masana badini, wato su ne tatattun wato asalin Sufaye. Wadanda suka fita daga Shari’a zuwa hakika, duk abin da Shari’a ta wajabta na Tsarki da Sallah da Azumi su ba wajibi ba ne a kansu, haka duk abin da Shari’a ta haramta na Zina da shan giya da aikata alfasha da dukkan masha’a ba haramun ba ne a kansu. Saboda su sun gama Shari’a sun shiga hakika da badini.

Bikin Sema

‘Yan Hakika su ne wadanda suka kai kololuwa a Sufanci, suka samu ilimin Ludani ta hanyar Kashafi, wanda ba a bayar da shi ga waninsu ba. Wannan ilimin shi suke kira Hakika, ko ilimin baɗini da suka dauko shi daga Allah kai tsaye ba tare da wani dan aike a tsakani ba. Har suke kaiwa matsayin Fana’i da ganin komai abu daya ne, komai ya zama Allah, babu banbanci tsakanin Allah da bawa, Allah shi ne bawa, bawa shi ne Allah.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Bin Jamil Zeno, Muhammad (1996). The Pillars of Islam & Iman. Darussalam. pp. 19–. ISBN 978-9960-897-12-7.
  2. Editors, The (2014-02-04). "tariqa | Islam". Britannica.com. Retrieved 29 May 2015.CS1 maint: extra text: authors list (link)