Suzi Barbosa
Suzi Barbosa | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
2 ga Maris, 2020 - 14 ga Augusta, 2023
3 ga Yuli, 2019 - 5 ga Faburairu, 2020 - Ruth Monteiro →
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 5 ga Yuli, 1973 (51 shekaru) | ||||||
ƙasa | Guinea-Bissau | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | University of Lisbon (en) | ||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Suzi Barbosa 'yar siyasa ce ta Bissau-Guinean, 'yar majalisa kuma mai gudanarwa na kwamitin 'yan majalisar mata na Guinea-Bissau.[1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Barbosa mai ba da shawara ce ga shigar mata cikin harkokin siyasa na ƙasa na Guinea-Bissau. Ta kasance ɗaya daga cikin masu rajin kare hakkin mata a Guinea-Bissau a tsakanin mata daga yankin Bafatá da suka kaucewa kada kuri'a a zaɓe idan ba a saka mata a cikin jerin 'yan takara ba. Ta yi nuni da cewa, “Guinea-Bissau tana da yawan al’ummarta galibi mata ne, kuma abin bakin ciki ne ganin cewa ba su da damar da maza suke da su, musamman wajen yanke shawara, da a ce suna da halin da ƙasar ke ciki ta fuskar tattalin arziki da kwanciyar hankali da ya bambanta.”[2][1][2]
Ta kasance wakiliya a taron farko na Da'irar Mata ta Majalissar Dokoki ta ƙasa a birnin Quebec a cikin shekarar ta 2017, wanda ya kunshi 'yan siyasa daga ƙasashen Faransa, da suka taru don inganta karfin shugabannin mata na duniya.[3]
Tun daga shekarar 2016, ta kasance Sakatariyar Harkokin Hulɗa da Jama'a ta Ƙasashen Duniya a Guinea-Bissau.[4]
A ranar 3 ga watan Yuli, 2019, ta zama Ministar Harkokin Waje. [5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Inspired by training on political participation, women from Bafatá region promise not to vote in political parties without women on the lists". UNIOGBIS (in Turanci). 2017-08-31. Retrieved 2017-11-21.
- ↑ 2.0 2.1 Shryock, Ricci (2020-03-23). "From The Battlefield To The Ballot Box". Trix-Magazine.com (in Turanci). Retrieved 2023-11-13.
- ↑ "Women who rule: Female politicians gather in Quebec City for leadership conference". Montreal (in Turanci). 2017-03-10. Retrieved 2017-11-21.
- ↑ "China has new projects in Guinea-Bissau and Cabo Verde". Macauhub (in Turanci). 2016-01-10. Archived from the original on 2022-05-20. Retrieved 2017-11-21.
- ↑ "Guinea-Bissau names gender-par cabinet after Ethiopia, South Africa". Africanews (in Turanci). 2019-07-05. Retrieved 2021-11-24.