Tanko Ishaya
Appearance
Tanko Ishaya | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mataimakin shugaban jami'a |
Tanko Ishaya Farfesan Najeriya ne a fannin ilimin na'ura mai kwakwalwa[1] kuma mataimakin shugaban jami'ar Jos.[2] An zabe shi a ofis a watan Disamba 2021.[3]
Rayuwar farko da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ishaya ya sami digiri na farko a fannin ilimin lissafi a jami'ar Jos a shekarar 1992 sannan ya fara koyar da lissafi a kwalejin aikin gona da ke Zuru ta jihar Kebbi. Ya kammala karatun digiri na biyu a fannin lissafi a Jami'ar Manchester a shekara ta 1997. kuma ya kammala Ph.D. a cikin Nazarin Kwamfuta a shekara ta 2001. Bayan ya dauki tsawon shekaru yana karantarwa a Jami'ar Hull (Scarborough Campus), ya koma garin Jos, inda daga baya aka kara masa girma zuwa Farfesa a fannin ilimin kimiyyar Kwamfuta (Computer Science) a shekarar 2012.