Taran Kano

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Taran Kano

Shura, wacce kuma aka fi sani da Taran Kano a ƙasar Hausa (ma'ana 'Majalisar Tara'), ita ce majalisar dokoki ta masarautar Kano. Madaidaicin ranar da aka kafa ta lamari ne na muhawara. Kamar yadda jaridar Kano Chronicle ta ruwaito, majalisar ta ƙunshi jami’ai tara ne, uku daga cikinsu suna sama da sarki, uku daga cikinsu daidai suke da sarki, uku kuma suna ƙarƙashin sarki.[1]

Mambobin Majalisar[gyara sashe | gyara masomin]

  • Galadima
  • Madaki
  • Alkali
  • Wambai
  • Makama
  • Sarkin Dawaki
  • Sarkin Bai
  • Dan-Iya
  • Chiroma

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Palmer, H. R (1908). Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland. 1908. Missing or empty |title= (help)