Jump to content

Ku kirkiri account domain taimaka ma Hausa Wikipedia. Kirkirar account kyauta ne. Idan kuma neman taimako ku tambaya a nan.

Teesdale, Victoria

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Teesdale, Victoria


Wuri
Map
 38°02′00″S 144°03′00″E / 38.0333°S 144.05°E / -38.0333; 144.05
Ƴantacciyar ƙasaAsturaliya
State of Australia (en) FassaraVictoria (en) Fassara
Yawan mutane
Faɗi 1,721 (2016)
Labarin ƙasa
Sun raba iyaka da
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 3328

Teesdale wani karamin gari ne a Golden Plains Shire, wanda yake kusa da birnin Geelong kilomitar 100 (ml 62) da ga yammacin cibiyar birnin Melbourne.<ref>https://en.wikipedia.org/wiki/Teesdale,_Victoria</ref> garin ya zamo wurin na masu bukakar gidan kan su musamman masu jeka ka dawo daga Geelong, sannan wuri ne da yake jawo masu saye da sayer da fili. a shekara 2006 garin yana da mazauna 1033 wanda kuma ya habaka zuwa 1479 a 2011 da kuma kidayar shekarar 2016 ta na nuni da mazauna 1721.<ref>Australian Bureau of Statistics (27 June 2017). "Teesdale (State Suburb)". 2016 Census QuickStats. Retrieved 2017-08-31. </ref> alamun garin na nuni da gari ne karami da ke arewacin babbar hanya wacce mazauna wurin ke kiran ta da 'Turtle Bend',ko kuma alamar karamin gini da rufin karfe a sifar kunkuru. Anbude ofishin aika wasika a garin Teesdale a 8 ga watan maris na shekara 1864<ref>Premier Postal History, Post Office List, retrieved 2008-04-11</ref> Anbude shagon saida magani a 13 ga watan disamba na shekarar 2013.