Teku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Teku
Paracas National Reserve, Ica, Peru-3April2011.jpg
subclass ofwater area, still waters, wuri Gyara
tributarymain stream, distributary Gyara
has listlist of seas Gyara

Teku wani ginshikin bigire ne wanda Allahu subhanahu wata'ala ya gina, sashi ne wanda ya kunshi duniyar ruwa da yake gudana a doron kasa. Teku ne ma'ajiyar duk wani ruwa da yake gangarowa ta kowanne bangare a fadin duniya.

Kodayake teku ta rabu gida-gida wato kananan teku zuwa kuma manya kamar irinsu tekun atlantika wato Atlantic ocean da kuma tekun maliya wato Red sea kasancewar teku nan ne matattarar duk wani ruwa, ta kunshi manya-manya halittun ruwa kama tun daga kifi zuwa wasu halittu na daban wadanda bamu sansu ba. Bayan haka dandanon ruwan teku yakasance mai gishiri-gishiri ne ba kamar yadda ruwan rijiya yake ba.

Masana ilimin kimiyya sun tabbatar da cewa inda ruwa ya mamaye a duniya yafi inda kasa ta mamaye. A bisa kididdiga inda ruwa ya mamaye ya kai kashi saba'in da biyar cikin dari (75%), amma inda kasa ta mamaye kwata-kwata kashi ashirin da biyar ne cikin dari (25%).

Amfanin Teku[gyara sashe | Gyara masomin]

Teku' ta kasance babban kundi inda dan adam ke amfani dashi a rayuwarsa, ana amfani da teku domin tafiye-tafiye acikin jiragen ruwa daga kasa zuwa kasa ko daga wata nahiya zuwa wata nahiyar.

Sannan kuma akwai hallitun ruwa da ake samu daban-daban kamar su kifi, dorinar ruwa, da dai sauransu, haka zalika man fetur shima duk daga teku ake samo shi da kuma irinsu gwala gwalai da dai abubuwa masu dimbin amfani ga Yan-adam

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Wannan ƙasida guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.