Terminus des anges
Terminus des anges | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2010 |
Asalin harshe | Larabci |
Ƙasar asali | Moroko |
Distribution format (en) | video on demand (en) |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
During | 86 Dakika |
Direction and screenplay | |
Darekta | Hicham Lasri (en) |
Marubin wasannin kwaykwayo | Hicham Lasri (en) |
External links | |
Terminus des anges (Turanci: Angels' Last Stop) fim ne da aka shirya shi a shekarar 2010 na Moroccan anthology fim wanda Mohamed Mouftakir, Hicham Lasri da Narjiss Nejjar suka jagoranta, wanda aka saki a cikin shekarar 2010.[1][2][3] Fim ɗin dai ya kunshi gajerun fina-finai guda uku ne, kowane daraktansa daban. An fara shi a bikin Fina-Finan ƙasa na Tangier.[4][5][6] Fim ɗin yayi magana akan batun AIDS.
Takaitaccen bayani
[gyara sashe | gyara masomin]An fara fim ɗin ne da tsakar dare a kan titin Casablanca, inda wata mata ba zato ba tsammani aka kamata da laifin karuwanci, bayan binciken 'yan sanda ya nuna cewa tana ɗauke da kwaroron roba. A kashi na biyu na fim ɗin Mohamed Mouftakir, matar farko ga wani mutum mai dauke da cutar kanjamau da ya kashe kansa, ta kalli wani faifan bidiyo da ya bar mata yana bayyana dalilansa na kashe kansa. Sashe na ƙarshe na fim ɗin ya ƙunshi matasa biyu da suka haɗu a karon farko kuma suna son yin soyayya. Matashin, wanda ya kasa yin zane-zane kuma mai mafarki, zai so yin hakan ba tare da kwaroron roba ba. Budurwar ta ki duk da jayayyar da ke tsakaninsu da juna. A ƙarshe, kwatsam, duk jaruman fim ɗin sun ƙare a ofishin 'yan sanda.
'Yan wasa
[gyara sashe | gyara masomin]- Sana Akroud
- San'a Alaoui
- Bensalah Bensalah
- Nadia Niazi
- Ismail Kanar
- Bouchra Ahrich
- Driss Roukhe
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Films | Africultures : Terminus des anges". Africultures (in Faransanci). Retrieved 2021-11-28.
- ↑ Angels' Terminal (in Turanci), retrieved 2021-11-28
- ↑ "TERMINUS DES ANGES" (in Faransanci). Retrieved 2021-11-28.
- ↑ "Narjis Najjar, Mohamed Mouftakir et Hicham Lasri s'attaquent au sida". Aujourd'hui le Maroc (in Faransanci). Retrieved 2021-11-28.
- ↑ BOUITHY, ALAIN. "Nejjar, Mouftakir et Lasri signent trois courts métrages sur le sida : "Terminus des anges" pour dénoncer préjugés et ignorance". Libération (in Faransanci). Retrieved 2021-11-28.
- ↑ "Festival National du Film - 11ème édition - Tanger 2010". CCM.