Jump to content

Terrence Mashego

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Terrence Mashego
Rayuwa
Haihuwa Mamelodi (en) Fassara, 23 ga Yuni, 1998 (26 shekaru)
Karatu
Makaranta Jami'ar Fasaha ta Tshwane
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Terrence Mashego (an haife shi a ranar 23 ga watan Yuni 1998) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Afirka ta Kudu wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kulob ɗin Cape Town City na Afirka ta Kudu da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu.

Aikin kulob/Ƙungiya

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mashego a Mamelodi, Gauteng.[1] Ya shiga ƙungiyar matasa ta Arcadia Shepherds a cikin 2006.[2] [3] Mashego ya halarci makarantar sakandare ta Bona Lesedi, inda ya kammala karatunsa a shekarar 2014.[4] [3] Ya halarci Jami'ar Fasaha ta Tshwane ta hanyar karatun wasanni daga 2016, yana hada karatu tare da yin wasa da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta su amma ya barta bayan watanni 8 kuma ya sanya hannu a ƙungiyar National First Division Mthatha Bucks. [3] Ya yi bayyana sau ɗaya a Bucks a cikin lokacin 2016–17 da bayyana 10 a cikin lokacin 2017–18.

Mashego ya shiga sabuwar kungiya ta National First Division TS Galaxy a shekarar 2018. Ya lashe Kofin Nedbank na 2018–19 tare da Galaxy bayan kulob din ya doke Kaizer Chiefs a watan Mayu 2019.[5]

A watan Oktoban 2020, Mashego ya rattaba hannu a kulob din Cape Town City na Afirka ta Kudu.[6]

Ayyukan kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Mashego ya samu kiransa na farko zuwa tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu domin buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da kasar Habasha a watan Oktoban 2021.[7] Ya buga wasansa na farko a Afirka ta Kudu a wasan da suka doke Habasha da ci 3-1 a ranar 9 ga watan Oktoba.

TS Galaxy

  • Kofin Nedbank : 2018-19[8]
  1. Sibanyoni, Buleyeni (16 October 2021). "Terrence Mashego inspirational rise to the top". New Frame. Retrieved 9 April 2022.
  2. "Terrence Mashego: Summary". Soccerway. Perform Group. Retrieved 9 April 2022.
  3. 3.0 3.1 3.2 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named new frame
  4. Sibanyoni, Buleyeni (16 October 2021). "Terrence Mashego inspirational rise to the top". New Frame. Retrieved 9 April 2022.
  5. Mothowagae, Daniel (19 May 2019). "Galaxybshock Amakhosi in Nedbank Cup final". City Press. Retrieved 12 October 2021.
  6. Ditlhobolo, Austin (9 October 2020). Terrence Mashego: Cape Town City confirm signing of TS Galaxy defender". Goal. Retrieved 9 April 2022.
  7. "Eric Tinkler hails 'dedicated' Terrence Mashego after first Bafana Bafana call-up". sport24. 28 September 2021. Retrieved 9 April 2022.
  8. Ratsie, Ofentse (12 October 2021). Terrence Mashego living his dream in the Bafana camp: 'This is a big moment for me' The Sowetan. Retrieved 9 April 2022.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Terrence Mashego at WorldFootball.net