Tsaka Mafi Girma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tsaka Mafi Girma
Scientific classification
KingdomAnimalia
PhylumChordata
ClassReptilia (en) Reptilia
OrderSquamata (en) Squamata
SuperfamilyGekkonoidea (en) Gekkonoidea
dangi Gekkonidae
Gray, 1825

Gekkonidae ( Geckos na gama-gari ) itace nau'in tsaka mafi girma a cikin nau'o'in tsaka dake akwai a duniya, wadda ta ƙunshi sama da nau'uka 950 idan aka kwatanta a cikin nau'ikan 64. Gekkonidae ta ƙunshi yawancin nau'in tsaka mafi yaɗuwa, ciki har da Tsaka ta gida ( Hemidactylus ), Tsakar tokay ( Gekko ), Tsaka ta wuni ( Pheluma ), tsakar makoki ( Lepidodactylus ), da dtellas (nau'in tsaka ce) sai kuma biological name ( Gehyra ). Ana samun kalar wannan nau'in tsakar kusan a kowane yanki na duniya kuma sun bambanta musamman a wurare masu zafi.

Halin halittar Hemidactylus tana ɗaya daga cikin mafi yawan (species-rich) kuma ta yaɗu a dukkan nau'ikan halittu masu rarrafe.

Burbushin halittunta[gyara sashe | gyara masomin]

Iyalin Gekkonidae memba ne na infraorder Gekkota, wanda da alama ya fara fitowa a lokacin Jurassic (shekaru 201-145 da suka wuce). Eichstaettisaurus schroederi an sanshi a matsayin ɗaya daga cikin misalan nau'ikan farko nq tsaka tun tale-tale. Membobin halittar Eichstaettisaurus suna nuna sauye-sauyen yanayin halittar da ke da alaƙa da hawa sama. An sanya Eichstaettisaurus a matsayin mai tushe gekkotan, amma ainihin darajar (taxonomic) ba ta da tabbas.

Irin nau'in Hoburogekko suchanovi da Gobekko cretacicus, wanda aka yi kwanan watan Albian - Aptian shekaru (shekaru miliyan 121-100) na zamanin Cretaceous, babu shakka mambobi ne na Gekkota. Ana tsammanin su mambobi ne na Gekkonidae, amma matsayinsu na (taxonomic) ba shi da tabbas saboda rashin cikar burbushin halittunsu.

Yantarogekko balticus itace farkon sananniyar gekkonid tsaka. An gano Y. balticus a cikin amber na Baltic wanda aka yi kwanan watan Eocene (shekaru 56-33.9 da suka wuce). Wannan nau'in ta kasance ƙanana, awonta bai wuce 20-22 mm. Y. balticus ta ƙara girma, maras raba sinadari na sikandire da raguwa amma mai ƙarfi da lambobi na farko, kuma ba tada fatar ido masu motsi. Tareda, cewa nau'in halittar jikin sun bambanta da dangin Gekkonidae, kuma suna nuna cewa Y. balticus na iya samun damar iya yin mannewa kamar Tsakar na zamani.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]