Jump to content

User:Abu-Ubaida Sani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

FINAFINAN HAUSA

Finafinan Hausa sun sami gindin zama na sosai a tsakanin al’ummar Hausawa. Tuni harkar shirya fina-finai ta zama wani ɓangare na rayuwar al’umma (Fage, 2004, Gidan Dabino, 2001). Harkar fina-finai ya kasance kasuwanci wanda jama’a da dama suka dogara a kansa domin samun abin sawa a baka. Sannan mutane da dama sun yi arziki ta dalilinsa. Wani abin burgewa dangane da harkar fim shi ne, rukunin masu sana’o’i da dama ne suke cin gajiyarsa. Sun haƙa da mawaƙa da taurari (‘yan wasa) da masu ƙaukar hoto na kati da na bidiyo da masu kwalliya da masu shagunan sai da kaset da masu shagunan tura waƙoƙi da fina-finai zuwa ga wayoyi da ma wasu rukunonin masu sana’o’i daban-daban. A taƙaice harkar fim na da tasiri a kan tattalin arziki matuƙa (Gidan Dabino, 2001; Aminu, 2004; Larkin, 2004; Chamo, 2004).

           A ƙaya ɓangaren kuma, fina-finan Hausa suna zaman figi-naka-na-figi-nawa ne tsakaninsu da al’adun Hausawa. Dalili kuwa shi ne, al’adun Hausawan na taka rawar gani cikin tsarin fina-finan. Yayin da a ƙaya ɓangaren kuma, su fina-finan ne ke jan akalar al’adun Hausawa zuwa wata ƙurya ta daban. Za a iya ganin hakan idan aka yi la’akari da yadda fina-finan suke yin tasiri a kan rayuwar al’umma. Sukan samar da sara da sababbin ƙabi’u da dama (Bunza, 2002; Iyan-tama, 2004; Ibrahim, 2004)

           Wannan aiki ya bi sawun tarihin samuwar wasan kwaikwayo a taƙaice. Sannan ya waiwayi shigowar wasan kwaikwayo na zamani zuwa ƙasar Hausa da kuma fara shirya fina-finan Hausa. Manazarta da dama sun gudanar da bincike game da lokacin da aka fara samun fina-finan Hausa. Sai dai sakamakon binciken manazartan yakan ƙan bambanta saboda raunin tarihi. Manazarta da suka yi tsokaci kan tarihin samuwar fina-finan Hausa a cikin ayyukansu daban-daban sun haƙa da; Yimi, (1981); gidan Dabino, (2001); Ali, (2004) da sauransu. Baya ga haka, aikin ya kawo waƙansu ƙabi’u da suka samu a dalilin fina-finan Haua. Muradin aikin ya ta’allaƙa ne a kan nuna waƙannan ƙabi’u ba tare da mayar da hankali kan yanke hukunci game da kyawu ko rashin kyawunsu ba.

           Bayan waƙannan, aikin ya waiwayi tasirin fina-finan Hasau (kamar sauran ɓangarorin adabin Bahausahe na zamani – zube da rubutacciyar waƙa), a kan rayuwar Bahaushe. Sakamakon yana nuni da cewa, adabin na mazaunin akala da ke sarrafa al’ummar Hausawa. Daga ƙarshe kuma aikin ya kawo wasu shawarwari game da hanyoyi ko matakan da za su iya sanya fina-finan Hausa su kasance masu taka-rawar-gani wajen ci gaban al’umma baki ƙaya.

Ma’anar Muhimman Kalmomi na Cikin Take

Fim: Fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da ke ƙauke da hotunan mutane, wato hotunan mata ko maza, yara ko manya ko kuma ma wanin mutane, wanda aka ƙauka ko kuma hanyar yin amfani da na’urar ƙaukar ta musamman, tare da bai wa mutane (kowannensu) damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko waninsa, a wani ƙan lokaci da aka keɓe wanda shi wasan kwaikwayo yake ƙauke da wani saƙo na musamman kan nishaƙi da gargaƙi da wa’azi da soyayya da tarihi ko wanin haka, zuwa ga al’ummar duniya (Kiyawa, 2013).

Ƙabi’a: Ƙabi’a na nufin halin mutum ko al’adarsa (Ƙaraye, da Yalwa, 2006). A wannar takarda, ƙabi’a ta ƙauki ma’anar duk wani hali na al’umma, tun daga magana, tafiya, sutura, cin abinci da ma sauran abubuwan da suka shafi rayuwa ta yau-da-kullum.