Tattaunawar user:Abu-Ubaida Sani
Barka da zuwa Hausa Wikipedia, Abu-Ubaida Sani! Mun ji daɗin gudummuwarka. Kuma ina fatan zaka tsaya ka ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimake ka ka fahimci Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:
- Gabatarwa
- Tutorial
- Cheatsheet
- Yadda ake rubuta muƙala
- Manufofin Hausa Wikipedia
- Shawarwari goma akan gyaran Wikipedia
Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial, ko kuma ka tambayeni a . Na gode. Em-mustapha t@lk 16:31, 26 ga Yuni, 2020 (UTC)
Wikipedia Pages Wanting Photos na Hausa Community
[gyara masomin]Muna gayyatan kudan shiga gasar WPWP Contest na Hausa Community!
Wikipedia Pages Wanting Photos na Hausa Community gasa ce ta duk shekara wanda editoci a Wikipedia daga Hausa Community User Group ke sanya hotuna a mukalolin da basu da ko keda karancin hoto articles. Wannan dan a inganta da karfafa amfani ne da dubannin hotunan da ake samu ne daga gasa daban-daban na hotuna da ake gudanarwa duk shekara, wanda Wikimedia community ke shiryawa a Wikipedia. hoto na inganta fahimtar mai karatu, da bayyana bayani, da sanya mukaloli suyi kyau. Gasar Kuma zata ba sabbin editoci da tsoffi damar inganta kwarewa, dan shiga samun kwarewa tuntube mu anan Emel.
Danna nan dan shiga gasa da Karin bayani..Em-mustapha t@lk 16:31, 26 ga Yuni, 2020 (UTC)
Tattalin Arziki a Bahaushen Tunani
[gyara masomin]Tattalin arizikin al’umma abu ne mai faɗi. Ya shafi dukkanin al’amuran da ke haɗuwa su ba da hoto ko bayani kan arzikin al’umma. Curarren furuci ne da ke da yalwa. Farfajiyarsa ya haɗe da abubuwa da suka shafi kasuwancin al’umma da sana’o’insu da dukiyoyinsu da kadarorinsu da kuma yadda suke cuɗanya da gudanar da rayuwa tare da waɗannan abubuwa da aka zayyana. Furucin tattalin arziki hatsin bara ne. Mika’il, (2015: 3) ya bayyana cewa: “Kalmomi guda biyu ne suka tayar da kalmar tattalin arziki, watau, “tattali” da “arziki.” Wannan na nuna cewa, sanin ma’anonin kalmomin biyu na da matuƙar amfani. Hakan ne zai ba da damar fahimtar gundarin ma’anar furucin (tattalin arziki). Kalmar “tattali” kamar yadda Auta (2006:194) ya bayyana: “... kalma ce mai nuna rainon wani abu har ya kai ga ya girma.” A ɓangare guda kuwa, ya bayyana ma’anar “arziki” da “... samun dukiya ko wani abin mallaka.” Yayin da aka nazarci waɗannan ma’anoni, ke nan tattalin arziki na nufin “renon dukiya ko wani abin mallaka mai amfani da tarisi ga ci gaban rayuwa ta hanyar yin amfani da dabarun tattali da adana da killacewa.” Bunƙasar tattalin arziki na faruwa ne yayin da abin mallaka ko dukiya ta haɓaka. Koma bayan haka kuwa, shi ake kira “daƙushewa ko karayar tattalin arziki.” Ƙumshiyar tattalin arziki na shafar abubuwa da dama a zamantakewar al’umma. Sun haɗa da: a. Kasuwanci b. Sana’o’i c. Fatauci d. Adana e. Tallafi Haɗakar waɗannan kuwa (da ma wasu makamantansu), a jimlace sun shafi “biɗa” ne da “tanadi.” Ci gaban tattalin arziki na iya kasancewa: (i) Na matakin mutum (ii) Na matakin al’umma ko ƙasa Tattalin arzikin matakin mutum ya shafi sukuni ko wadata ko tajircin ɗaiɗaikun jama’a a cikin al’umma. Shi kuwa na matakin ƙasa ya haɗa da arziki da wadatar ƙasar na gaba ɗaya. Bisa haka ne ma Ibrahim ya bayyana ma’anar tattalin arziki ta hanyar la’akari da matsayi ko gurbin gwamnati ga sha’anin tafiyar da tattalin arziki. Ya ce: ... tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa ɗan’adam domin samar da muhimman abubuwan buƙatu da rarraba su ga jama’a masu buƙata. Ibrahim (1981:5) Kafin a ce tattalin arziki ya bunƙasa kuma ya samu gindin zama, dole sai al’umma (wadda ake magana a kanta) ta kasance mai fasahar sarrafawa da samar da abubuwan buƙata na rayuwar yau da kullum. A bisa wannan tunanin ne Umar ya gina ma’anar tattalin arziki. A ciki ya bayyana sarrafa abubuwan rayuwa a matsayin ginshiƙin tattalin arziki. Ya ce: “Tattalin Arziki tsari ne na sarrafa wasu abubuwa domin samun abubuwan rayuwa.” Umar (1983:5). Yayin da ake ce an samu bunƙasar tattalin arziki, ana nufin cewa: a. Akwai ci gaba a hada-hadar kasuwanci, b. Akwai sabin fikirori da fasahohi a ɓangaren sana’o’i, sannan ana samun riba mai gwaɓi, c. Arzikin al’umma ya kai ga bunƙasar da suna iya dogaro da kansu, d. Masu ayyukan yi su suke da rinjaye yayin da marasa aiki suka kasance ƙalilan, sannan e. Talauci ya yi ƙaranci a tsakanin al’umma.
(Abu-Ubaida Sani (talk) 22:43, 25 Satumba 2020 (UTC))
"Kofa:Adabi"
[gyara masomin]Assalamu Alaikum, Abu-Ubaida Sanida fatan kana lafiya. Muna jinjina maka akan kirkirar shafin Kofa:Adabi a harshen Hausa. Sai dai naga alamu kamar an dauko research ne na wani gaba daya aka sanya. Da fatan cewa kuna sane da dokokin hakkin mallaka (copyright). Kuma ya kamata a sanya ainihin littafin ko research din a sashin bibliography ko kuma external link idan shafin yanar gizo ne. Godiya, da fatan zaka tsaya cigaba da bada gudummawa.Patroller>> 22:47, 28 Satumba 2022 (UTC)
- Wslm
- Binciken nawa ne. Ni na rubuta takardar.
- Sannan ta yaya zan iya magana da jami'an Hausa na Wikipedia? Akwai shawarwari da nake son bayarwa game da matsalolin rubutun Hausa da ke kan shafin. Abu-Ubaida Sani (talk) 05:55, 23 ga Maris, 2023 (UTC)