Jump to content

Wikipedia:Yadda ake rubuta muƙala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Yadda Ake Rubuta Muƙala
Za ku iya koyon yadda ake rubuta muƙalar Insakulofidiya a nan.


Wikipedia:

Barka da zuwa Wikipedia!. Ku fahimci rubuta sabuwar muƙala a cikin Wikipedia abu ne mai sauƙi.

Gabatarwa

Muna yi muku lale marhaban da zuwa Wikipedia ta harshen Hausa tare da fatan za ku haɗa hannu da mu domin bunƙasa ta. Da farko yana da kyau ku fahimci Wikipedia ta Hausa wani kundin ilimi ne da ake son tattara dukkan muhimman bayanai na ilimi na ɗan'adam (wato insakulofidiya). Wikipedia ta tattaro ilimin ɓangarori da dama wanda ya shafi dukkan ilimin ɗan'adam na da, da na yanzu, na kusa ko na nesa; mai kyau da mara kyau.

Wikipedia ta Hausa ta bambanta da wasu kafofin sada zumunta da taɗi kamar facebook ko WhatsApp da sauran ire-iren hanyoyin sadarwa na zamani. Wikipedia ta Hausa ana rubuta ta ne a kan manhaja da babu son rai, sannan ba manufar Wikipedia ba ne tallata wata haja ta wata aƙidar siyasa ko rayuwa ba, sannan ba a tallace-tallacen ra'ayoyi da kuma kayan kasuwanci a cikinta. Har ila yau, Wikipedia ta bambanta da jarida ko mujalla, domin ba hadafinta ba ne ba da labaran yau da kullum ba, ba kuma ƙamusu ba ce, domin ba manufarta ba ne ba da bayanin ma'anonin kalmomi ba. Ita Wikipedia ta Hausa babban hadafinta shi ne tattara gundarin ilimi a wuri guda a cikin harshen Hausa domin amfanar da al'ummar da ke amfani da harshen; ɗalibai, malamai da ma sauran masu bincike.

Neman muƙala a Wikipedia

Kafin ku fara rubuta sabuwar muƙala a Hausa Wikipedia yana da kyau ku fara bincikar ko an riga an rubuta wannan muƙalar. A halin yanzua akwai muƙaloli 49,658 a kan Hausa Wikipedia, to tana iya yiwuwa wadda kuke nema an riga an rubuta ta. Kamar yanzu in kana son ganin muƙala a kan birnin Kano sai ku duba a Special:Search ku sa "Kano"; kuna fara rubutawa za ta fara zubo muku da muƙkalolin da ke da wannan suna. Idan muƙkalar tana nan, to za ku ga sunan ya fito shuɗin rubutu kamar haka: (Kano). Idan kuma babu muƙalar to za ku gan ta a jan rubutu kamar haka: (Misali).

A lokacin da za ku bincika sunan yana da kyau ku tuna duk sunayen da wurin ke amfani da shi, domin wasu abubuwa za ku ga suna da sunaye da yawa. Idan wurin yana da suna fiye da ɗaya, za a iya karkatar da ɗayan sunan domin ya je zuwa ga shafin saboda mutane da suka sa duka sunayen su isa zuwa ga shafin cikin sauƙi. Misali, jihar Legas ana kiranta "Legas" ko kuma "Lagos". To za iya aje muƙkalar a "Legas" sai a tabbatar "Legos" kuma an karkatar da shi zuwa ga shafin. To duk lokacin da mutum ya sa kowane sunan zai isa zuwa cikakken shafin.

Tattara asalin bayanai

Kafin ku rubuta mukala yana da kyau ku fara nazartar asalin bayananku. Domin kamar yadda aka fada Wikipedia ta Hausa ba wurin sadarwa na zamani bane inda kawai zaka iya rubuta abinda kake so. Kamar idan kuna son rubuta mukala akan "Kankana" to abinda ya kamata shine ku fara nazartar littattafai ko kuma mujallu sanannu da suka yi rubuta akan kankana, sai ku dora bayaninku akan hakan. Idan kuna son rubuta tarihin wani dan siyasa ko malami ko masanin kimiyya da dai sauransu, sai ku fara bincikar kamar shafukan BBC, VOA da jaridun kasa domin ku ga me aka rubuta akan wannan mutumin, sai ku dora bayanan ku akan hakan. Idan ku ka fara rubutun to duk wani bayani mai muhimmanci sai ku bada madogarar binciken ku; wato inda kuka samo shi. Zaku iya ganin karin bayani akan madogarar bincike a shafin Wikipedia:Tutorial/Bada madogarar bincike.

Abubuwan lura

A lokacin da kuke shirin fara rubuta mukala akan Wikipedia ta Hausa, da kuma lokacin da kuke cikin rubutun da kwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku lura dasu sosai. Na farko ku fahimci Manufofin Wikipedia sannan ku karanta Shawarwari goma da a ka fidda anan. A kasa, ga karin bayanin su:

Talla

Ba'a kafa Wikipedia ta Hausa ba domin talla kuma ya zama wajibi masu amfani da ita su kiyaye. Talla, ko ta wani dan siyasa ko malami ko mawaƙi da kuke ƙauna ko kuma wani kasuwanci, wani magani ko fahimta ta addini ko siyasa ko ta harkokin rayuwa duk ba'a amince ba da su. Wikipedia wuri ne kawai domin tattara ilimin dan adam da kuma gabatar da shi ta hanyar da zai amfani mutane kuma ya isa gare su cikin sauki. Editocin da suka nace a wajen yin talla ko wace iri, za'a iya blocking din su, domin kare manufofin Wikipedia ta Hausa.

Satar fasaha

Ba za ku iya kwafo rubutu daga wani wuri ba ba tare da izini ba. Duk mukaloli da hotuna da ke akan Wikipedia ana bada shine a lasisin gama-gari ta yadda kowa zai iya amfani da abubuwan dake cikinta, da sarrafa su da yaɗa su gaba, shi yasa ya zama wajibi duk abunda za a dora akan Wikipedia shima ya zama yana da lasisin gama gari. Saboda haka, Wikipedia ta Hausa bata ajiye rubutu ko hoto, mai motsi da mara motsi wanda bashi da cikakken izini daga mai haƙƙin mallakar shi. Saboda haka yana da kyau mu fahimci kwafo rubutu daga wasu shafukan yanar gizo, ko a litattafai ko jaridu da mujallu ba tare da izini ba yana da matuƙar hadari kuma laifi ne. Da zaran an tabbatar rubutun an kwafo shine daga wani guri ba tare da izini ba to za'a goge shine da gaggawa daga Wikipedia ta Hausa tare dayin gargadi ga mai aikata hakan. Nacewa akan kwafo rubutu ba tare da izini zai iya sa ayi blocking din account din mutum domin kare Wikipedia ta Hausa da kuma dokokin hakkin mallaka na ƙasar Amurka (inda injinan dake tafiyar da Hausa Wikipedia suke). Wikipedia ta dauki Haƙƙin Mallaka da matukar muhimmanci kuma ya zama tilas akan kowane mi gyaranta da sha'awar ci gabanta ya kiyaye hakan.

Bidiyoyi na tutorial (Kirkiran mukala)

Wadannan bidiyoyi ne da zasu taimaka ma Hausawa sanin hanyoyin da zasu bi wajen gudanar da sauye-sauye da kuma gyara a Hausa Wikipedia, Bidiyoyin zasu taimaka ma sababbin editoci sanin hanyar da zasu bi wajen koyan editin cikin sauki a Wikipedia. Kowanne bidiyo a cikin nan yana da darasin da yake koyarwa, idan kana da bukatan karin bayani ko kuma neman wasu bidiyoyi, zaka iya ma wannan magana a shafin shi na tattaunawa Anasskoko. Wadannan bidiyoyin dake kasa bidiyoyi ne da zaka koya yanda ake kirkiran shafi/mukala wato (article) a Wikipedia.


Idan kai mutun ne ma'abocin karance-karance zaka iya duba PDF na koyan yanda zaka kirkira mukala a Hausa Wikipedia, ka sauke manhajar PDF din a cikin wayarka.



*Manufofi Biyar *Shawarwari akan gyaran Wikipedia *Yadda ake rubuta muƙala *Rubutu a mahangar da ba son rai *Ingancin tushen bayanai