Kofa:Adabi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
yan matan hausawa suna gada

Taqaitaccen Tarihin Wasan Kwaikwayo Xanjuma (2004) ya ce, wasan kwaikwayo na farko a doron qasa ya samu ne tun zamanin Annabi Adam. Bayan da ‘ya’yansa biyu suka yi faxa a kan mata, sai xaya ya kashe xaya. Wanda ya yi kisan ya shiga cikin damuwar yadda zai yi da gawar. A nan Allah ya turo da mala’iku a cikin siffar hankaki. Hankakin suka yi faxa har xaya ya kashe xaya. A nan hankakan da ya yi kisan ya tona rami ya busne xan uwansa da ya kashe. Wanda daga nan ne ‘yan Adam suka kwaikwayi wannan qaramin wasan kwaikwayo ta hanyar busne ‘yan uwansu a duk lokacin da suka rasu. Samuwar Fim a Qasar Hausa Tarihin fara fina-finan Hausa (harkar da ta fi kafuwa a Kano) yana da dangantaka ta kai-tsaye da tarihin fara fina-finai a Nijeriya baki xaya (Ali, 2004). Fim kuwa a Nijeriya ya samu tun kafin samuwar Nijeriya a matsayin qasa xaya. An fara fim na farko a Nijeriya qarqashin kulawar Herbert Macauly a shekarar 1903 (Alfred, 1979; Ali, 2004). A xaya vangaren kuma, ba a haxa Kudu da Arewa (a matsarin qasa xaya – Nijeriya) ba sai a shekarar 1914. Yayin da kuma aka ba wa Nijeriya ‘yancin kai a shekarar 1960 (Isichei, 1997; Douglas, 2004). Tsakanin shekarar 1903 zuwa 1970 an samu yunqurin shirya fina-finai da dama. Ali, (2004) ya kira su da rukunin fina-finan farko na ‘yancin kai. Masu hannu a cikin waxannan fina-finai sun haxa da Nuhu Ramalam da Adamu Halilu. Bayan nan kuma, kamfanoni sun xauki nauyin shirya wasu fina-finai. Daga cikin waxannan fina-finan akwai ‘Shehu Umar’ da ‘Amadi’ da ‘Salla Durba’ (Ali, 2004). Fina-finan Hausa kuwa kamar yadda ake kallon su yanzu, an fara su ne tsakanin shekarar 1980 zuwa 1984 a Kano (Gidan Dabino, 2001). Fage, (2011) ya ce, fina-finan Hausa waxanda aka fi sani da fina-finan Kanawa sun fara samun karvuwa ne wajen 1990. A wannan lokaci an sami qungiyoyin fim guda uku da suka haxa da (i) Gwauron Dutse, da (ii) Karate, da kuma (iii) Gyaranya, waxanda kuma duka sun wanzu ne a Kano. Fina-finan farko da aka fara gudanarwa qarqashin waxannan qungiyoyi su ne: ‘Hukuma Maganin ‘Yan Banza’ da ‘Yan Xaukar Amarya’ da kuma ‘Baqar Indiya’. Waxanda suka xauki nauyin waxannan fina-finai su ne masu xaukar nauyi na farko (first producers); Alhaji Hamisu da Muhammad Gurgu da kuma Sani Lamma (Gidan Dabino, 2001; Ali, 2004). Zagari Game da Fina-finan Hausa Idan aka yi la’akari da muhawarar masana da manazarta a kan alfanu da koma baya da fina-finai suke samar wa, za a iya cewa, fina-finan Hausa sun kasance hanjin jimina, akwai na ci a kwai na zubarwa. Haqiqa fina-finan suna taimakawa ta vangarori da dama. Ali, (2004) ya ce, a tsawon qarnuka biyu da suke wuce, samuwar fina-finan Hausa shi ne hanyar havaka tattalin arziki mafi girma da ya samu ga al’ummar Hausawa. Sai dai duk da haka, manazarta irin su; Iyan-tama, (2004) da Alkanawy, (2000) suna ganin samuwar finafinan Haua yana da illa ga al’ummar Hausawa. Wannan aiki ya kalli vangarorin biyu kamar haka: Amfanin Fina-finan Hausa Samuwar fina-finan Hausa ya zo da ci gaba ga al’ummar Hausawa ta fannoni da dama waxanda suka haxa da: i. Samun Aikin Yi: Rukunin masu sana’o’i da dama suna cin gajiyar sana’ar shirya fina-finai. Waxannan rukunnai na masu sana’o’i sun haxa da masana harkar fim, da marubuta da masu xaukar hoto da masu shagon sayar da kaset da ma wasu masu sana’o’i daban-daban. Lallai ta nan za a iya cewa wannan ci gaba ne ga al’ummar Hausawa (Dumfawa, 2002; Malumfashi, 2002; Ali, 2004). ii. Bunqasa Al’adu da Adabi: Fim hanya ce da take taimakawa wajen bunqasa al’adu da adabin Hausa. Wani abin mai da hankali a nan shi ne, fim na taka rawar gani wurin tallata al’adu zuwa ga baren al’ummu. Fina-finan Haua da dama sukan shiga hannun wasu al’ummu waxanda ba Hasauwa ba da suke zaune a nan gida Nijeriya, har ma da na qasashen waje (Nwuneli in Ali, 2004). iii. Faxakarwa: Haqiqa fim hanya ce ta faxakar da al’umma game da lamura da dama. Akwai fina-finan Hausa da jigoginsu ke faxakarwa kan abubuwa kamar illar zafin kishi, ko qarshen mai munafurci, ko illar zato da zargi, ko cututtuka da ma wasu da dama makamantan waxannan (Chamo, 2004; Yakub, (2004). iv. Sada Zumunta: Fim xin Hausa na taimakawa wajen qulla zumunci musamman tsakanin taurarin fim. Baya ga haka akwai fina-finai da suke jan hankali zuwa ga amfani da dacewa da buqatar sada zumunta (Chamo, 2004). v. Koyar da Tarbiyya: Akwai fina-finan Hausa da dama da suke xauke da jigon tarbiyya. Irin waxannan fina-finai suna faxakarwa zuwa ga biyayya ga iyaye (kamar fim xin Linzami da Wuta), ko bin miji (kamar fim xin Aljannar Mace) da sauransu (Chamo; 2004; Yakub, 2004). vi. Nishaxantarwa: Haqiqa ana nishanxantuwa daga kallon fina-finan Hausa. Akai fina-finan Hausa da dama da aka gina jigonsu kan nishaxi. Babban tauraro a vangaren fina-finan Hausa na nishaxi shi ne marigayi Rabilu Musa wanda aka fi sani da Xan Ibro (Chamo, 2004; Yakub, 2004). Illolin Fina-finan Hausa Masu iya magana suna cewa: “Kowane allazi da nasa amanu!” Haka abin yake ga fina-finan Haua. Manazarta da malaman addini sun daxe suna nuni ga illoli da suke tattare ga fina-finan Hausa. Abubuwan da ake qorafin kansu sun haxa da: i. Vatar da Al’ada: Za a iya kwatanta fina-finan Hausa da maganar Bahaushe da ke cewa: “Ana yabonka salla ka kasa alwala.” Duk da ikirarin da ake yi na cewa fina-finan Hausa suna havaka al’ada, wasu na ganin ko kusa ba haka abin yake ba. Sun tafi kan cewa, a maimakon fina-finan su taimaka wajen havaka al’adun Hausawa, sai ma suna qara daqushe su ne kawai. Fina-finan Hausa na daqushe al’adun Hausawa ta hanyoyin da suka haxa da: (a) Harshe: Wato yawan amfani da Ingausa tare da fifita harshen Ingilishi a kan na Hausa. (b) Sutura: Fifita suturun wasu al’ummu kamar Turawa da Indiyawa sama da na Hausa. (c) Muhalli: Watsi da muhallin Bahaushe tare da fifita na wasu al’ummu sama da na Hausawan (Chamo, 2004; Al-kanawy, 2004). ii. Shgaltarwa: Akwai manazarta da suke kallon fina-finan Hausa a matsayin hanya na shagaltar da al’umma daga wasu ayyuka da sha’anoni da suka fi dacewa. Wannan ya fi zama abin magana musamman idan aka kalle shi daga vangaren addini wanda bai zo da wasa ko shagala ba (Al-kanawy, 2004; Iyan-tama, 2004). iii. Fanxarewa: Akwai manazarta da suke kallon fina-finan Hausa a matsayin masu ruxi zuwa ga fanxarewa. Wannan na faruwa ne musamman idan aka duba irin shigar taurarin fina-finan waxanda suka ci karo da addini da kuma al’ada. Sannan tsaurin ido ga na gaba da sauran halayen banza da ake nunawa a cikin fina-finan (Al-kanawy, 2004; Iyan-tama, 2004) iv. Cuxanya Tsakanin Maza da mata: Xaya daga cikin manyan abubuwan da suka fi jan hankali, waxanda kuma suke jawo sukar fina-finan Hausa shi ne cuxanya tsakanin maza da mata. Wannan ya kasance musamman idan aka kalli lamarin ta fuskar addini (Iyan-tama, 2004). v. Waqa: Waqa ta kasance a cikin fina-finan Hausa tamkar gishiri a cikin miya. Manazarta na kallon hakan qalubale ne musamman idan aka yi la’akari da matsayin waqa a Musulunci. Manazarta da dama bayan waxannan sun tafi kan cewa fina-finan Hausa suna taka rawar gani matuqa wajen gurvata al’adun Hausawa. Manazartan sun haxa da: Xangambo, (2013) wanda ya ce, a wani fim xin idan da za a cire harshen da aka yi Magana a cikinsa (Hausa) to babu yadda za a iya danganta shi da Hausawa. Guibi da Bakori (2013) sun tafi kan cewa, telebishin na xaya daga cikin hanyoyi mafi sauqi da suke vata tarbiyyar Hausawa. Kiyawa, (2013) ya kawo wasu hanyoyi waxanda yake ganin ta nan ne fina-fina-finan Hausa suke ruguza al’adun Hausawa. Waxannan hanyoyi su ne: i. Sun ci karo da koyarwar addinin Musulunci ii. Rashin kyakkyawar wakilci ga al’adun Hausawa iii. Lalata tarbiyyar yara da matasa iv. Cusa baqin al’adu marasa nasaba da Addini da al’ada v. Nakasa ruhin auratayya vi. Samar da varna vii. Dogon buri (Kiyawa, 2013).