Jump to content

Wikipedia:Tutorial/Shafukan tattaunawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gabatarwa Rajistar account Yadda ake gyaran Wikipedia Yadda ake mahadar shafi Bada madogarar bincike Shafukan tattaunawa Manufofin Wikipedia Karin bayani  
Bidiyo na Turanci da yake bayanin shafukan tattaunawa

Shafukan Tattatunawa wasu shafuka ne masu muhimmanci da suke ba editocin Wikipedia damar magana da junansu domin tattauna muhimman al'amurra da kuma yadda za'a inganta Wikipedia.

Shafukan tataunawa na mukala

Kowace mukala a Wikipedia tana da shafin tattaunawa. Ashafin tattaunawa ne za'a iya tattauna ita kanata mulkalar domin gano hanyoyin inganta ta ko kuma domin warware gardama a tsakanin editoci akan wani abu dake cikin mukalar.

Shafin tattaunawa na edita

Kowane edita da yayi rajistar account yana da shafin dake hade da sunan sa domin tattaunawa da sauran editoci. Idan kayi rajistar account, zaka iya zuwa shafinka na tattaunawa kai tsaye ta hanyar Special:MyTalk. Domin saurin gane kowane rubutu da kuma wanda yayi shi a shafukan tattaunawa, kowane edita zai iya rubuta sunansa {wato username). Zaku iya yin hakan cikin sauki ta hanyar amafni da alamar "~" guda hudu (~~~~)

Amfani da guda hudu, shine zai samar da sunanku da kuma cikakkaken kwanan wata da kuma lokaci, kamar haka:

  • Misali, rubuta ~~~~ shi zai bada sunan mai rubutun da kuma kwanan wata (Suna, 00:39, Nuwamba, 2024 (UTC))

A wani lokaci za'a iya bukatar suna kawai banda lokaci. Za a yi amfani da alamar ~ guda ukku domin samun hakan:

  • Misali, rubuta ~~~ shine zai bada(Sunan mai rubutun kawai),

Idan ana son kwana wata kadai, sai ayi amfani da guda biyar:

  • Misali, rubuta ~~~~~ shine zai bada cikakken kwanan wata kamar haka: (00:39, Nuwamba, 2024(UTC)).

Daidaita rubutu a shafukan tattaunawa

A lokacin da ake magana tsakanin editoci a shafin tattaunawa, yana da kyau a daidaita rubutu domin saukin fahimta. Za'a iya daidaita rubuta ta hanyoyi fda dama kamar ta hanyar afmani da alamar star:

* Na daya
** Na biyu
*** Na ukku
**** Na hudu
***** Na biyar
Yin hakan shi zai bada:

  • Na daya
    • Na biyu
      • Na ukku
        • Na hudu
          • Na biyar

Sannan za'a iya amfani da alamar hash,

# Na daya
# Na biyu
# Na ukku
# Na hudu
# Na biyar

Wanda hakan shi zai bada lambobi kamar haka:

  1. Na Biyu
  2. Na biyu
  3. Na Ukku
  4. Na hudu
  5. Na biyar

Za'a iya kuma bi da rubutu ta hanyar amfani da alamar ":" kamar haka:

:daidaito na farko
::daidaito na biyu
:::daidaito na ukku
::::daidaito na hudu

Wandda shine zai bada:

daidaito na farko
daidaito na biyu
daidaito na ukku
daidaito na hudu

Zaku iya ganin karin bayani game da shafukan tattaunawa a Shafukan Tattatunawa.


Ci gaba zuwa Manufofin Wikipedia