Wikipedia:Tutorial/Gyaran Wikipedia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gabatarwa Rajistar account Yadda ake gyaran Wikipedia Yadda ake mahadar shafi Bada madogarar bincike Shafukan tattaunawa Manufofin Wikipedia Karin bayani  

Gyaran Wikipedia abu ne mai sauki.

Ana iya gyaran Wikipedia da kowace irin na'ura da aka hadata da yanar gizo, kamar komfuta, wayar hannu da kuma matsakaitansu irin su tablet. Sannan a Wikipedia dakwai muhimman hanyoyi biyu na yin gyaran. Akwai ta hanyar gyara rubutun kai tsaye (Wikitext) akwai kuma ta hanya da ake Kira da (Visual editor).

Yadda ake gyaran

A shafin kowace mukala dakwai malatsin "Edit" ko kuma "Gyara" wanda da zarar an latsa shi, zai bada damar gayaran mukalar domin inganta ta ko kuma fadada ta. A shafin gyaran, dakwai hanyoyi da yawa na sarrafa ainihin gundarin rubutun cikin sauki, da kuma dubawa domin tabbatar da komai yayi daidai kafin adanawa.

Gajeran bayanin gyara

Riga gani

Bayan ka gama duk gyaran da zaka yi, yana da kyau kayi amfani da maballin "Show preview" wanda zai nuna maka gyaran da kayi kafin a adana. Amfani da wannan maballin yana da muhimmanci sosai, domin zai nuna maka duk wani kuskure da kayi, ko abin da baka sa ba.

Maballin "Show preview" da ake amfani domin gani gyara kain a adana.

Adana gyara

Ci gaba da Yadda ake mahadar shafi