Jump to content

Wikipedia:Tutorial/Manufofin Wikipedia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gabatarwa Rajistar account Yadda ake gyaran Wikipedia Yadda ake mahadar shafi Bada madogarar bincike Shafukan tattaunawa Manufofin Wikipedia Karin bayani  

Wikipedia insakulofidiya ce, (Kundin Ilimi)

Wikipedia insakulofidiya ce da ta tattaro ilimin bangarori da dama wanda ya shafi dukkan ilimin dan adam. Ba manufar Wikipedia bane tallata wata haja ta :wata akidar siyasa ko rayuwa, bu kuma hadafinta bane tallacen tallacen ra'ayoyi da kuma kayan kasuwanci ba. Wikipedia ta bambanta da jarida ko mujalla, :domin ba hadafinta bane bada labaran yau da kullum ba, ba kuma kamus bace, domin ba manufar ta bane bada bayanin ma'anonin kalmomi ba.

Wikipedia ana rubuta ta daga mahangar da ba son rai

Editocin Wikipedia suna kokarin yin bayanin al'amurra daga mahangar da ba son rai a cikinta, da kuma baiwa kowane al'amari hakkinsa. Wannan yana nufin :dukkan muƙaloli dake a cikin Wikipedia ya zama tilas a rubuta su daga mahangar adalci, mahangar da ba son rai ko kuma fifita wani al'amari saboda wani :dalili. In kana rubuta muƙala, ka rubuta iya sahihan bayanai da aka riga aka rubuta a ingantattun littatfai ko jaridu da makamantansu, sanna kuma ka :bada inda ka samo wannan bayanan daga karshen muƙalar.

Wikipedia ta kowace, da kowa zai iya gyarawa kuma yayi amfani da abubuwan da ke cikinta

Dukkan abun da aka rubuta a Wikipedia yana karkashin lasisin CC BY-SA 3.0 wanda yake ba kowa damar iya amfani da rubutun, saboda haka babu wani edita :daya da yake da hakkin mallakar wata mukala ko wani shafi akan Wikipedia; ko da shi kadai ya rubuta shi duka.

Masu gyara Wikipedia (Editoci) dole suyi mu'amala da juna cikin girmamawa

Domin samun damar yin aiki cikin jin dadi da zaman lafiya, dole ne kowane editan Wikipedia ya girmama dan uwanshi, kuma ya maida ansa ko martani ta :hanyar amfani da tattausan lafuzza a yayin da ake muhawara. Babu maganar cin zarafin juna, kuma ko da yaushe ka kyautata zato akan danuwanka edita

Zaku iya ganin karin bayani akan manufofin Wikipedia a shafin Wikipedia:Manufofi biyar.


Ci gaba zuwa Karin bayani