Jump to content

User:Usman Ahmad Isa/Draft

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Rana na samar da kaso 99.97% na dukkan karfi/kuzari da tsarin duniya da sararin samaniya (earth-atmosphere) suke amfani da shi. A kowace dakika, rana tana samar da kalori 56 x 1026 (calories) na karfi/kuzari wanda daga ciki duniya take karbar kason kalori 2.5 x 1018 kadai.

Gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

KASAFIN ZAFI TSARIN EARTH-ATMOSPHERE

Rana wani kwallo ne mai haske wanda yake dauke da gases. Tana da zafi da ya kai akalla 6000°c bisa ma'aunin celcious. Rana ta na samar da energy ne a sigar electromagnetic wave wanda yakanyi tafiyar 299,300km a cikin dakika daya.

Duk da cigaba haskowar rana zuwa duniya zamu ga cewa daukacin zafinta bai canja ba. Hakan ya na faruwa ne idan ya kasance adadin karfinta dake shigowa zuwa earth yayi dai dai da adadin da earth-atmoshere suke aikewa zuwa space. Yin hakan shi yake samar da daidaito tsakanin hasken rana da yake shigowa da kuma zafin da earth-atmosphere suke aikewa zuwa duniyar sararin samaniya (space). Wanna shi ake kira da "Kasafin tsarin Duniya da Sararin Samaniya".

Kasafin Tsarin Zafin Duniya da Sararin Samaniya[gyara sashe | gyara masomin]

A kalla kaso na unit 35 a cikin unit 100 na hasken rana da ya ke tahowa ana aikewa da shi kai tsaye zuwa space. Hakan yana faruwa bisa dalilin:

  • Girgije zai aike da kaso 27units.
  • Dutsen kankara da yake a doron duniya ze aike da 02units.
  • Atmosphere zata aike da kaso 06units.

Jumilla: 35units.

Wannan kaso 35unit da ake aikewa kai tsaye zuwa space baya dumama earth-atmosphere saboda baya ma ko isowa garesu.

Ragowar kaso 65unit na energy atmosphere da kuma doron duniya suke zuke shi.

  • Atmoshere na zukar 14unit.
  • Doron kasa na zukar 51unit.

Jumilla: 65unit.