Usman Mu'azu (jarumi)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Usman Mu'azu furodusa ne jarumi a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood.[1]. Fin-finan sa sannu ne wanda baza'a taba mantawa dasu ba a masana'antar. Sun yi tashe Kuma sun faɗakar har yanzun ana kallon su a maimaita kallo , yayi amfani da Manyan jarumai musamman a fim dinsa Mai suna "Dan Marayan Zaki"

Takaitaccen Tarihin Sa[gyara sashe | gyara masomin]

Cikakken sunan sa shine Usman Mu'azu jarumi ne Kuma furodusa ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood.[2]

Masana'antar fim[gyara sashe | gyara masomin]

Dalilin da yasa ya shiga Masanaa'ntar shine tun yana makaranta yake kallon fina finan amurka da indiya irin yadda suke yada Al'adunsu suke fadakarwa SE shima yai sha'awan ya fara a kasar sa. Ya shiga masana'antar ya zama jarumi daga Nan ya zama furodusa.ya shiga masana'antar a shekarar 2004, a yanzun yayi fina finai sama da dubu. Yayi zamani a masana'antar ya Dade a masana'antar Yana fim

Fina finan sa.[3]

  • Hedimasta
  • karangiya
  • Yaki da jahilci
  • Ga duhu ga haske
  • Sarauta
  • ga fili ga Mai Doki
  • Maza da mata
  • Dan marayan Zaki
  • garba gurmi
  • hangen nesa
  • Ummi Adnan
  • Ashabul kahfi
  • Wuta da aljannah
  • Bashin gaba
  • Lantana

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://aminiya.ng/dalilin-da-na-shiga-harkar-fim-usman-muazu/
  2. https://fimmagazine.com/tag/usman-muazu/
  3. http://hausafilms.tv/producer/usman_muazu