Jump to content

Waina Da Miyar Taushe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

YADDA ZA'A HADATA

Mataki Na Farko[gyara sashe | gyara masomin]

Dafarko zaki jika shinkafar tuwo watau farar shinkafa ta kwana idan baki samu damar haka ba ki jikara koda na 2hrs ne, sannan kisa yeast kibada akai maki markade, idan an dawo ki kara yeast kisa a guri dumi ko rana domin ya tashi.[1]

Mataki Na Biyu[gyara sashe | gyara masomin]

Sannan kizo ki fere kabewa ki Dora a wuta idan tadahuki sauke ki murjeta ko ki daka. Sannan kizo ki hada kayan miya ki markada ki sa mai a wuta idan yayi zafi ki zuba markadaddun kayan miya ki soya idan sun soyu ki tsaida[2] ruwa daidai yanda kikeson miyar ta kasance.

Mataki Na Uku[gyara sashe | gyara masomin]

Saiki zuba maggi da salt sai spices da kabewar da jika daka, sannan ki yanka alayyahu da albasa ki zuba ki barsu na minti 5 saiki sauke miyarki yayi.[3]

Mataki Na Hudu[gyara sashe | gyara masomin]

Saiki dauko kwabinki idan ya tashi kisa baking powder da salt da sugar ki soya a tander.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://cookpad.com/ng/recipes/6701699-waina-da-miyar-taushe
  2. https://managarciya.com/day-30-ramadan-yadda-za-ki-haƊa-miyar-taushe
  3. https://m.youtube.com/watch?v=9W2DOOCgmN0