Waki'ar 19th april
TARIHIN WAKI'AR 19TH APRIL A KATSINA
[gyara sashe | gyara masomin]Ya Waki'ar 19th April ta wakana?
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin watan disamba na shekarar 1990 wata mujallar barkwanci mallakin Gwamnatin Tarayya mai suna Lolly ta yi ta wallafa wani zanen ɓatanci mai muni da cin zarafin Manzon tsira (S) da Musulunci baki ɗaya. Ganin wannan yasa wasu daga cikin Musulmi ɗalibai da ke a manyan makarantu suka yunkura dan ganin an ɗaukar ma abin mataki da yi masa iyaka da hukunta masu laifin, amma Gwamnati ta yi biris.
[gyara sashe | gyara masomin]Ganin ba a ɗauki wani mataki ba yasa sai kuma wata Mujallar mai suna Fun Times ta sake buga kalaman wani mai suna Orlando, wanda yayi maganganu marasa daɗi da siffanta Annabi da wasu munanan ɗabi'u tare Annabi Isah ɗan Maryam (A.S), kuma yace; a alƙur’ani ya gani (an buga labarin a watan disamba 1990, sashi na 2 fitowwa ta 67 a shafi na 21 mai taken TATTAUNAWA TA MUSAMMAN).
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan wannan cin zarfin an ɗauki tsawon wata 3 babu wani mataki daga ɓangaren hukuma har ma daga Musulmin ƙasar, haka Malamai da sarakunan gargajiya. Wannan yasa Shaikh Zakzaky (H) da almajiransa suka ɗauki matakin kare Annabi (S). Bayan gudanar da Muzahrori daga wasu garuruwan da 'yan’uwa suka yi to a garin Katsina ma anyi sai dai a nan abin ya zo da cikas kamar yadda zaku ji nan gaba:
[gyara sashe | gyara masomin]'Yan’uwa sun haɗu a wata makarantar firamare da ke ƙofar ƙaura ida suka yi sahu zuwa ofishin da wannan mujalla ta ke kuma suka kwaso ta suka ƙona, kuma suka sake hawan sahu suka koma babban Masallacin Juma'a na garin inda aka rufe a nan.
[gyara sashe | gyara masomin]
Faruwan hakan ke da wuya kau, sai gwamnan wancan lokaci wato John Madaki ya tara manema labarai a ranar Alhamis 4 ga watan Afirilu, 1991 inda ya sanar dasu matakin da ya ɗauka, kuma ya ambata ƙarara cewa; “DUK RANAR DA MALAM YAKUBU DA ALMAJIRANSA SUKA KARA YIN ZANGA-ZANGA TO IDAN BAYA SON YA MUTU, TO YA GUDU YA BAR ƘASAR, IN BA HAKA BA MU ZAMU JE GIDANSA MU KAMO SHI MU KAISHI FILIN POLO MU HARBESHI A GABAN JAMA'A”.
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan yanke wannan hukunci, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya cika da murna da farin ciki, wanda har sai da na tare dashi suka ga hakan a zahiri, ko gezau, ga wanda ake shirin kashewa. Wannan ya nuna irin zallar sallamawar Shaikh Yakubu Yahaya ga addinin Allah da jagoransa (H).
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 16 ga watan Afrilu, 1991, ita ce ranar da Shaikh Zakzaky (H) ya tako Katsina inda ya tabbatar ma mai ƙudirin kisa (John Madaki) cewa sai dai a mutu in dai akan kare Annabi ne. Bayan ya taya Shaikh Yakubu Yahaya murna da wannan matsayin da sai Annabawa da A'imma ke samu kuma ya roƙi Allah Ya maisheshi damshen Shaikh Yakubu Yahaya.
Sayyid Zakzaky (H) Ya ƙarƙare jawabinsa da jan kunne ga John Madaki da kuma ayyana ranar juma'a mai zuwa da ranar da za a sake fitowwa jerin gwanan tir da kalamansa idan ya isa ya hana. Sannan duk Masoyan Annabi (S) to ya fito dan nuna baƙin ciki da wannan cin zarafin ga Manzon Rahma (S). A ranar 17, ga watan Afrilu, 1991, Shaikh Zakzaky ya koma garinsa bayan tattaunawa da 'yan jarida a Katsina.
A tsakanin 17 zuwa 18bga watan na Afirilu ba abinda kake gani a Katsina sai sabbin jami'an tsaro da ake ta kawowa daga jahohi daban-daban, in taƙaice maku dai an kwashe kusan kwana 3 cur ana jibge jami'an tsaro, ko ina ka duba sune.
A ranar 19 ga watan Afrilu, 1991 tun da safiyar wannan rana ta juma’ar ko wane ɗan'uwa yana cikin murna da farin cikin zai samu Shahada. Su kuwa ɓangaren jami'an tsaro an raba masu aiki. Mr. S. U Thilza SP, shi da mutanansa 'yan sandan kwantar da tarzoma suka kasu gida biyu, kashin farko suka riƙa yawo cikin gari kusa da Masallaci. Kashi na 2 kuma suna a ofishinsu na C.P.S hanyar Nagogo Road kuma wasu jami'an ne ƙarkashin umarnin shugaban ofishin 'yan sanda Aƙilu Garba Bakori, bisa titin kofar marusa kuma Mr. Barnabas Mamman ne da tawagarsa... Haka dai suka ci gaba da karkasuwa a cikin garin na Katsina.
Misalin ƙarfe 12:00 dai-dai kamar yadda ya saba Shaikh Yakubu yayi bankwana da mahaifiyarsa da Matarsa da 'ya'yansa da dangisa, ya fito yana fara'a ko'ina ya wuce faɗi ake ALLAHU AKBAR, ga Hurras tare da shi kowane ɗauke da rigar da ake kira NASRA KO SHAHADA.
Bayan gama Sallar juma'a da jawabin Shaikh Yakubu Yahaya sai aka hau sahu duk da cewa tun kafin ma a hau sahu jami'an tsaro tun sun fara dukan mutane da korarsu ƙarshe ma ana sa sahu su kuma suna harba tear gas. haka dai aka ɗaga aka nufi 'Yar'aduwa inda can ma wasu tawagar jami'an tsaron ne, su ma suka ci gaba da antayo hayaki ba ƙaƙƙautawa. Zafin wannan tear gas ya sa wasu suma ciki har da mata da yara. Anyi ƙoƙarin yin magana dasu da ankarar dasu cewa; wannan fa jerin gwanon lumana ne amma sam suka tubure suka cigaba da dukan mutane. Akwai wanda ke riƙe da tutar gaba M. Abdurrashid Mai ƙarfi sun ta bugunsa har sai da ya kai kasa sannan wani ya amshi tutar cikin 'yan'uwa aka ci gaba tafiya, shima suka rufar masa haka dai aka ci gaba da ɗauki ba daɗi har dai aka kammala muzaharar a gidan waya kuma aka ƙona butun butumin John Madaki. Wannan kaɗan kenan daga abinda ya faru a ranar.
Bayan wannan ta faru to kuma garin Katsina ya shiga yanayin da tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba lallai an ci gaba da bin 'yan'uwa gida-gida ana kamawa da kuma duka, kai ko ganinka akayi da kamala ta addini ko ba ɗan harka bane to lallai zaka ɗan-ɗana kuɗarka. Abubuwa da dama sun faru kafin da bayan wannan wanda lallai ba zasu ambatu a wannan rubutu ba.