Yakubu Yahaya Katsina
SHAIKH YAKUB YAHYA KATSINA
[gyara sashe | gyara masomin]ya kasance daya daga cikin manyan almajiran Sheikh ibrahim Zakzaky a birnin katsina. Yana daga cikin almajiransa na farko-farko tun bayan fara da'awar Sheikh zakzaky a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria.
[gyara sashe | gyara masomin]Yakub Yahya, ya kasance Malami mai ilimi tare da aiki da shi, kuma ana masa lakabi da ‘Gwarzon kare martabar Manzon Allah’ wanda wannan suna Sheikh Zakzaky ne ya rada masa shi tun a waki’ar 19th April da ta faru a shekarar 1991 a birnin Katsina, kuma ita ce waki’a ta farko da aka fara a tarihin harkar Musulunci karkashin jagoran Sheikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky
Mutanen yankin da Shaikh Yakub ke wakilta dai sun kasance suna matukar son sa da kaunarsa, kuma an san shi da kyakkywar alaka da mutane da son hadin kai tsakanin al’umma hatta wadanda ba ’yan shi'a ba.
Shine mutum na farko cikin mabiyan Sheikh Zakzaky da Gwamnatin Nigeria ta fara afkawa da mutanansa da yake wakilta a Da’irar Katsina, hakan ya shahara ta yadda kowa ya san shi da wannan zaluncin da aka yi masa na Gwamnati a wancan lokacin da su ’yan’uwa Musulmi almajiran Sheikh Zakzaky din suke wa lakabi da Waki'ar 19th april
TARIHIN HAIHUWARSA
Gari, Shekara Da Wajen Da Aka Haifi Shaikh Yakub Yahya Katsina.
An haifi Shaikh Yakub Yahya Katsina a ranar 15 ga watan Rajab,1376 Hijiriyya (1955 Miladiyya) a Unguwar Adoro da ke gab da Unguwar-madawaki a tsakiyar birnin Katsina.
Maihaifinsa Alhaji (Malam) Yahya, haifaffen ƙaramar hukumar Rimi ne ta Jihar Katsina. Malama Maryam ita ce mahaifiyarsa, 'yar asalin ƙaramar hukumar Mani ɗin Jihar Katsina ce. Ita 'ya ce ga Malam Zubairu, shi kuma Malam Zubairu ɗa ne ga Malam Aliyu, dukansu haifaffun Ƙaramar hukumar Rimi ta jihar Katsina ne.
IYALANSA.
Yanzu haka Shaikh Yakubu Yahya yana da Mata biyu da 'ya'ya shatakwas: Tara Maza, Tara Mata. Ya aurar da guda goma (tsakanin Maza da Mata), Yanzu Saura 8 tare da jikoki sama 40 da tattaɓa kunne 5.
KARATUNSA.
A farkon farawa Malamin ya fara Karatun Allo a wajen Mahaifinsa Malam Yahaya a matakin farko na Ilimi, daga baya ya koma wajen wasu Malamai abokan mahaifinsa ya ci gaba da karatun nasa na Allo. Malaman da yayi karatun Allo a wajensu sun haɗa da: Malam Sani, Malam Adamu Unguwar Sararin Kuka da kuma Malam Alti a Unguwar gidan waya. Bayan rasuwar Malam Alti, Shaikh Yakub Yahya ya koma da karatun nasa na Allo kacokaf a wajen Malam Salisu Mutumin Jan-geru wanda yake zaune a Unguwar Sha'iskawa a wancan lokacin, daga bisani ne kuma ya koma da karatunsa wajan Malam Aliyu mai 'Yar Makaranta a anguwar ma-dawaki duk a cikin birnin Katsina. Da karatun nasa ya kara nuna, har wayau shaikh Yakub Yahya ya sake komawa da karatunsa kacokaf a wajen Mahaifinsa Malam Yahya, inda ya ɗora da karatun Littattafan Addini.
HAZAƘARSA A MAKARANTA
Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya kasance Mutum mai ƙwaƙwalwa da hazaƙar gaske, duba da yadda ya yi karatu na Muhammadiyya tun yana ƙarami har zuwa girmansa, wannan ya sa ƙwaƙwalwarsa ta wuce Makarantar Firamare har ma da Sakanadire a lokacin, sai kawai kaitsaye ya wuce Makarantar gaba da sakandire. Shaikh Yakub ya kasance yana ɗaukar matsayin farko 'Distanction' ne a ajinsu, kuma bai taɓa samun abinda ake cewa 'Carry over' a duk Makarantun da yayi ba, duk da cewa akwai darussan turanci a cikin tsarin abin da yake karanta, kai a taƙaice ma dai Shaikh Yakub Yahya sai da ya rubuta ƙamus na turanci da na Larabci nashi na ƙashin kansa saboda nacewarsa a kan Yaruka guda biyu; Larabci da Turanci. Saboda tsananani kaifin kwakwalwarsa da haddace abubuwa nan-da-nan, wannan ya sa ma 'yan ajinsu suka sa masa suna ‘Computer’.
A rayuwar wannan bawan Allah ma'abocin jajircewa, akwai darussa da al'umma musamman Matasa za su koya. Misali: Matasa su kula cewa ba komai ne za su koya ba a aji, domin shi Shaikh Yakub bai zauna a ajin firamare ba amma ya koyi turanci dai-dai gwargwado, ya iya ya kuma kware da harshen Larabci. Ya samu wannan karatuttuka ne akasari a wajen bincike da yawan Karance-karance musamman na Litattafai, jaridu, Mujallu, jin labarai, karanta littattafai irin na koyi da kanka kamar yadda ya faɗa da bakinsa.
SANA'O'INSA.
Ganin cewa karatu ba Sana'a ba ne, sai mahaifinsa ya fara dora shi a kan sana'o'i tare da sauran 'Yan’uwansa. Shaikh a janibinsa, ya fara da Sana'ar Dinkin Hula, domin dogaro da kansa. Daga nan kuma Shaikh ya ƙara da yin wasu sana'o'in daban-daban waɗanda suka haɗa da: Saida kwan Zabbi, Saida Yalo/Gauta/Ɗata, Saida Rake, kai abun burgewa har ma da yin Dako a kasuwa a biya shi. Shaikh Yakub bai tsaya nan ba har Sana'ar ginin Ƙasa ya yi, da Noma, Trader da kuma sana'ar gyaran wuta (Electrician) wanda kuma shi ne sana'arsa ta baya-baya a samartaka kafin Malanta ta janyeshi a shekarar 1969.
An naƙalto wannan tarihi ne daga Shafin Shaikh Yakub Yahya Katsina Shafin Shaikh Yakub Yahya Katsina
https://w.wiki/CZ9vhttps://w.wiki/CZ9v