Jump to content

Wale Aboderin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wale Aboderin
Rayuwa
Haihuwa 1958
Mutuwa 30 Mayu 2018
Yanayin mutuwa  (Gazawar zuciya)
Karatu
Makaranta Kwalejin Gwamnati, Ibadan
Clifton College (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan jarida

Gbadebowale Aboderin (1958 – 30 ga Mayu 2018) ɗan jarida ne ɗan Najeriya, ɗan kasuwa kuma mai kula da harkokin wasanni, wanda har ya rasu ya kasance shugaban kamfanin buga littattafai na Punch, wanda mahaifinsa ya kafa. Vanguard wanda ya bayyana shi a matsayin ginshiƙin aikin jarida, [1] ya yi karatu a Kwalejin Gwamnati, Ibadan da Kwalejin Clifton, kafin ya sami horon jirgin sama a Makarantar Flying Burnside-Ott. A wasanni, ya kasance shugaban kungiyar kwallon kwando ta jihar Legas kuma mataimakin shugaban kungiyar magoya bayan kwallon kwando ta Najeriya [2]. Aboderin ya rasu ne bayan tiyatar zuciya da aka yi masa a Legas [3] Archived 2018-07-29 at the Wayback Machine.Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode na cikin wadanda suka yi wa iyalansa ta'aziyya.[4] Archived 2020-02-20 at the Wayback Machine