Wikipedia:Hausa Wikimedia Data Support/Review committee
SHIRIN INTANET DATA SUPPORT NA HAUSA WIKIMEDIA
Wannan shiri ne na Hausa Wikimedia Foundation na taimakon membobin gidauniyar da intanet data ko kuma kudin siya ga wanda suke da buƙata domin a ci gaba da bunƙasa Hausa Wikipedia da kuma ƙara samun gogewa a wurin inganta Wikipedia ta Hausa dama wasu sauran projects na Gidauniyar Wikimedia.
Wannan shafin yana dauke da bayanin kwamitin da Wikimedia Hausa ta kafa domin tantance applications na Data Support. Idan kuna son shiga komiti din zaku iya applying a Review Committee Application form. Amma ku fara karanta ƙa'idojin shirin kafin bada application.
---
Kwamiti
[gyara masomin]Wikimedia Hausa tare da taimakon Gidauniyar Wikimedia tana gabatar da shirin Data Support da ke tallafa ma masu bada gudummuwa tun a shekarar 2023. Saboda tasirin shirin, a shekarar 2024 an faɗaɗa shi tare da kuma inganta shi ta hanyar sabbin tsare-tsare da kuma ƙara yawan mutanen dake amfana da shirin. Domin ci gaban shirin har yanzu, muna neman masu bada gudummuwa su shigo cikinsa domin kara tabbatar da inganci a wajen tafiyar dashi.
Muna neman masu bada gudummuwa da suke da ƙwarewa a bada gudummuwa a Wikipedia musamman ta Hausa ko wasu projects na Wikimedia domin haɗa tunani wuri guda a bunƙasa shirin. Membobin Kwamitin zasuyi aiki da ya danganci yin bita, aunawa tare da tattaunawa akan applications na masu shiga shirin Data Support. Har ila yau, zasu zama masu bada gudummawa ta hanyar bayar da ra'ayi game da tafiyar da shirin Data Support program ko kuma kawo sabbin tsare-tsare da zai inganta shirin.
Membobin Kwamitin (wanda volunteer work ne) zasu yi aiki daga Satumba zuwa Disamban shekarar 2024. A Disambar 2024 za'a yi bitar shirin ga baki daya domin fahimtar inda aka sa a gaba da kuma nasarorin da aka samu ko akasin haka. Cikakken rohoton shirin a wannan lokacin shi zai bada damar fahimtar me ya kamata ayi a gaba.
Lokacin application
[gyara masomin]An fara amsar application a ranar Lahadi, 18 ga watan Augusta. Za'a rufe amsar application a ranar Lahadi, 25 ga watan Augusta. Lokacin application sati daya ne.
Ka'idojin application na Kwamiti
[gyara masomin]- Dole ne mutum ya zama yana da account a Wikipedia ta Hausa.
- Dole ne mutum ya zama yana da account a Wikipedia ta Hausa na aƙalla shekara guda.
- Dole ne mutum ya zama cikakken memba na Hausa Wikimedians UserGroup.
- Dole ne mutum ya zama baya aiki na musamman da wani UserGroup ko a Nijeriya ko a waje.
- Dole ne mutum ya sani cewa shi ba zai iya applying na Data Support ba a lokacin da yake a cikin Kwamitin.
Ina son shiga wannan kwamitin
[gyara masomin]Idan kun cika ƙa'idojin shiga Kwamitin, zaku iya applying a nan: Review Committee Application form kafin ranar rufewa, 25 ga watan Augusta.
Karin bayani
[gyara masomin]Za'a sanar da membobin kwamitin a watan Satumba kuma zasu fara aiki a watan. Domin neman ƙarin bayani zaku iya rubuta saƙo zuwa ga data.supportwikimediahausa.org.