Jump to content

Wikipedia:Hausa Wikimedia Data Support

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

SHIRIN INTANET DATA SUPPORT NA HAUSA WIKIMEDIA

Wannan shiri ne na Hausa Wikimedia Foundation na taimakon membobin gidauniyar da intanet data ko kuma kudin siya ga wanda suke da buƙata domin a ci gaba da bunƙasa Hausa Wikipedia da kuma ƙara samun gogewa a wurin inganta Wikipedia ta Hausa dama wasu sauran projects na Gidauniyar Wikimedia.
Akwai wasu sharudɗa da za'a kiyaye a wurin wannan request, kamar haka:

  1. Ku tabbatar kunyi login da account dinku na Wikipedia a lokacin aika request.
  2. Ku tabbatar kun bada gudummuwar edit mai muhimmanci a Hausa Wikipedia.
  3. Ku tabbatar baku amshi grant (ko open grant application) daga wurin Gidauniyar Wikimedia ba ko kuma da wasu usergroups ba.
  4. Inda aka amince da request dinku na data support, ba zaku iya ƙara neman wani ba har sai bayan wata biyu.
  5. Ku amince da dukkan sharudɗan wannan shirin.

Karin bayani: Idan an amince da request dinku, ku karanta wannan shafin domin sanin yadda zaku amshi taimakon.

Hajjo30[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman data support ne domin na cigaba da dagewa a Inganta wikimedia, musamman a wiktionary, wikidata da sauransu. Samun support zai Kara sa na dage sosai a matsayi na mace wanda daliba ce mai jiran agaji Kafin na samu data don shiga yanan gizo musamman Wikipedia. Samun wannan data ya kamata a dunga bada shi musamman ga mu mata saboda a karama na kwazo domin mu kara dagewa. Idan na samu wannan data zai karamun kwazo kuma ya taimaka mun rage radadi a tsadar rayuwa da ta data da ake fama da ita a sub sahara ta afrika

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina kirkiran shafi, da kuma Inganta shafuka don amfanin masu karatu

HK RIGASA2[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Saboda Karin karfin gwaiwa domin bada gudunmawa a sashin Hausa na Wikipedia don karfafa wannan bangare don Hausa ta bunkasa. Musamman a wannan bangare na Hausa. Wadda shine daya Daga cikin yare mafi girma a bangaren nahiyar Hausa. Don haka wannan tallafi zai taimaka matuka Dan ganin mun bada gudunmawa a wannan sashi na Hausa Wikipedia. Wannan data support din zai taimaka mana sosai. Tare da karfafawa Dan haka zaitai maka sosai ina alfahari da Kasan cewa ta na daya Daga cikin wannan gidauniyya. Mun gode.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Nayi adit musamman a bangaren common

Mr. Snatch[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman data support ne sabida inganta ayyuka na a Wikipedia hausa, domin samun damar yin bincike sosai game da Wikipedia foundation, duba da irin cigaban da ake samu ayanzu a Wikipedia hausa, Hausa Wikipedia wurine Wanda yakamata akoda yaushe yazama kana bincike sosai domin samun muhimman bayanai da zasu Kara inganta shafin Wikipedia hausa, musamman idan muka duba yadda yaren hausa yake yaduwa a duniya baki daya, akwai abubuwa da yakamata ace ansansu da yaren hausa kuma dole mune zamu bada lokacin mu muyisu tare da gudunmawar Wikipedia foundation.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Nayi gyararraki sosai a wannan lokaci musamman a kirkirarrun shafuka.

Muhammad Idriss Criteria[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan data support ɗin ne saboda zai taimaka min wajen cigaba da inganta Hausa Wikipedia da kuma fassara muƙaloli daga harshen Turanci zuwa Hausa, Insha Allah. Ga wasu jerin muƙalolin dana fassara daga farkon watan Mayu zuwa yau, 👇👇👇 https://xtools.wmcloud.org/pages/ha.wikipedia.org/Muhammad%20Idriss%20Criteria/0/noredirects/all/2024-05-01/2024-06-01 https://xtools.wmcloud.org/pages/ha.wikipedia.org/Muhammad%20Idriss%20Criteria/0/noredirects/all/2024-05-01/2024-06-01

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ni gaskiya nafi karkata ga fassara muƙaloli daga harshen Turanci zuwa Hausa da kuma yin edits a wikidata. Ga jerin muƙalolin dana fassara 👇👇👇 https://xtools.wmcloud.org/pages/ha.wikipedia.org/Muhammad%20Idriss%20Criteria/0/noredirects/all/2024-05-01/2024-06-01

Pharouqenr[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina nema wannan data support din domin manufofi da dama misali, Saboda in samu damar yin edits masu kyau kuma masu ma'ana da kuma bada gudummawa sosai domin ganin cewa mutane da yawa sun ampana da abinda na rubuta da hannuna, kuma hakan zai bani damar kirkirar wasu sababbin articles da yawa idan na samu wannan dat support din. Haka zalika idan na samu wannan tallafin zai taimaka man wajan samun kwarin gwuiwa in cigaba da bada gudummawa.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na kirkiri articles da dama kamar "Capacitor, Arsenal, Diode" da saurasu

Apdoull[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ni dalibi ne a jami'ar federal university Dutse, jigawa state Kuma Wikipedia editor ne, wasu lokutan nakan rasa data din yin aiki sakamakon lamuran da sha'anin makaranta. Toh hakan Yana janyo koma baya akan gudunmaawar da nake bayarwa ga Wikipedia. Samun tallafin datan zai taimaka sosai wajen inganta gudun mawata ga Wikipedia. Ina gyaran articles ne wato (editing) Kuma nayi editing din articles da Daman gaske.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Nayi gyare-gyare sosai a articles da dama masu yawan gaske.

Abdurra'uf Uthman[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ena neman data support sabida samun tallafi ko kuma kwarin guiwa wajen bada gudummuwa a shafukan Hausa Wikimedia baki daya. Gudummuwan sun hada da kirkire-kirkiren muqaloli a wikipediar Hausa, da kuma ingata wasu da aka riga aka kirkira, sannan kuma bada gudummuwa wajen sauran fanni na Wikimedia irin su Wikidata da sauran su.

Wasu lokutan sabida rashin samun damar shiga yanar gizo a dalilin rashin datar na ja a samu rauni wajen bada gudummuwa, sannan kuma ita support din ko yaya take yana kara bada kwarin gwiwa wajen ayyukan wikipedian baki daya. Na gode.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

A matsayi na na editor, ena jajircewa wajen bada gudummuwa ta hanyar muqaloli da kuma ingata wasu muqalolin da aka riga aka kirkira, sannan ena bada gudummuwa iya gwalgwado a wikidata da sauran su.

A Sulaiman Z[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan data support ne domin na kara samun kwarin gwiwa wajen bayar da gudummawa ta a gyare-gyaren Wikipedia da yan uwanta kamar su Wiktionary da wikiqoat a Yaren Hausa domin ganin ta samu inganci da karɓuwa sama da sauran yarima. Duk da cewa muna yin wannan aiki ba wai don a biya mu ba sai domin manufar yada ilimi ga al'umma baki daya. To amma na tabbata cewa wannan wata hanya ce wadda zata kara zaburar da duk wani mai yin gyara a Wikipedia.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ga link na waɗansu daga cikin mukalolin da na kirkira https://xtools.wmcloud.org/pages/ha.wikipedia.org/A%20Sulaiman%20Z/0/noredirects/all/2024-03-01/2024-06-01

Sannan ga link na wadanda na yi masu gyara https://ha.wikipedia.org/wiki/Musamman:Contributions/A_Sulaiman_Z

Haweey7575[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina buƙata wannan support ɗin domin na ci gaba da bunƙasa Hausa Wikipedia da kuma ƙara samun gogewa da koya ma mata 'yan uwa na hanyoyin da zasu koya su ƙware don inganta Wikipedia ta Hausa dama wasu sauran manhajoji na Gidauniyar Wikimedia. A matsayi na admin ta mace ta farko wannan zai ƙara samun na dagewa don ganin wikipedia ta Hausa ta cigaba da samun ƙarbuwa da ingantuwa a wurin ɗalibai mata da maza a wuraren zaman mu, da wuraren aiyuka.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na ƙirƙira shafi a wiktionary mai suna "zubar da ciki", wannan shafin ya tsaro ta yanda harda sauti na saka masa, da Manazarta da mahaɗa.

Mustysummy[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Don ci Gaba da editing da inganta Wikipedia a Bangaren Hausa don Amfanin sauran Jamaa masu binciki akan Wikipedia Don rashin data Yana kawo mani tsaiko wurin editing Na Wikipedia Saboda Akwai lokacin da zan so yin editing Mai yawa to rashin data Sai ya hana ni gamin da tsadar rayuwa dake Akwai a Nigeria Don yada harshen Hausa akan Wikipedia Don yada al'adun Hausa da sanin fitatun mutanen su Idan Na samu data support zan yi kokarin yin editing Mai yawa a Kullum

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Jami'r California, Irvin

A'isha A Ibrahim[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Hakika a matsayina na mace kuma edita ta Hausa Wikipedia, ina mai neman wannan tallafin ne domin na kara samun damar zage damtse a fannin inganta Wikipedia. Kasancewar wannan ita ce hanya wadda za a ɗan kara karfafa mana guiwa duk da cewa kowa yasan muna yin wannan aiki ne domin gina al'ummar mu, haka kuma kamar yadda ake cewa mace ita ce uwar al'umma. Sannan ba a iya Hausa Wikipedia ba hatta a irin su Wiktionary da wikidata ina bayar da gudummawa ta.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Wannan shine link wanda yake kunshe da dukkan gudummawar da nake bayarwa a Hausa Wikipedia https://ha.wikipedia.org/wiki/Musamman:Contributions/A%27isha_A_Ibrahim

Hafeez gaiwa[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina Neman wannan data support ne saboda na Kara samun karfi guwa da zan bada gudun muwa a hausa Wikipedia da kuma in gata man kala ina so in ci gaba da bada gudun muwa sosai . Kuma zamuci gaba da bada gudun muwa a Hausa Wikipedia ko da bamu daga cikin wadda zasu samu Data support, Amma wannan data support zan taimaka ma editors sosai wajan ganin sun bada gudun muwar da duk ta kamata a Hausa Wikipedia


Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Adesegun fatusi Data Analysis C++ Compiler

Dev ammar[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Saboda samun tallafin data da zai taimaka wajen gyara Wikipedia da kuma rubuta sabbin articles a Hausa Wikipedia. Samun tallafin zai kara mani karfin gwiwa wajen gyara articles da kirkirar sabbi, sakamakon da Computer nake aiki kuma tana shan data sosai. Na samu data support a baya wanda hakan ya taimaka kwarai da gaske wajen gyara articles da dama, na samu nasarar gyara articles dubu ukku da dari biyar a cikin wata Shidda wanda hakan ya samu ne kawai ta dalilin data Support da na samu.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na kirkira articles da dama a Hausa Wikipedia kadan daga cikin su sune: 1. Annabi Sulaiman https://ha.wikipedia.org/wiki/Annabi_Sulaiman 2. Uche Okeke https://ha.wikipedia.org/wiki/Uche_Okeke 3. Veyvey, Swis https://ha.wikipedia.org/wiki/Vevey 4. El Paso, Texas https://ha.wikipedia.org/wiki/El_Paso,_Texas 5. Fort Worth, Texas https://ha.wikipedia.org/wiki/Fort_Worth,_Texas 6. Jerin Kauyukan Jihar kwara https://ha.wikipedia.org/wiki/Jerin_Kauyukan_dake_jihar_Kwara 7. Sheikh Albani https://ha.wikipedia.org/wiki/Sheikh_Al-Albani

Wadanda nake so na kirkira a nan gaba sun hada da:

1. Giza, Egypt 2. Rossetti, Egypt.

Isah muhammad[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Saboda In Kara inganta dakuma Samu kwarin gwiwar yin Sabo dakuma gyaran a cikin Wikipedia, Kuma Zan Kara Samu kwarin gwiwar Na Tura wa abokaina Suma suy fassara bayani, dakuma Karin hadin gwiwar da abokanan fassara a Wikipedia, Wikipedia tana samuwa kyauta ga duk wanda ke da haɗin yanar gizo, wanda ke sanya ta zama hanyar dacewa don samun bayanai na farko da bincike. Labaran Wikipedia sau da yawa suna haɗuwa, suna ba masu amfani damar sauƙin kewaya tsakanin batutuwa masu alaƙa da samun fahimtar gabaɗaya kan wani batu.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Gyra dakuma kirkiran Sabon fassara bayani

Nura Bello[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan tallafin na Data support domain zai bani damar cigaba da yin editing a shafin Wikipedia na Hausa domin cigaban Al'adatar mutanen arewacin Nigeria Domin habaka harshen Hausa domin cigaban Al'adatar Hausawa wadda ke samun cigaba a cikin kasashen Duniya tun daga kasashen Africa da amurka da Asiya da kasashen larabawa Wanda hakan zai taimaka sosai Gurin isar da sakon Al'ummar Hausawa Domin yin zozo zo da sauran yarukan Duniya.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina cikin wadan da sukayi Gyara acikin tarihin sarkin katsinan Gusau Wanda Yake a shafin Wikipedia Hausa.

Abbahofficial1438[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Domin cigaba da bunkasa wannan Gagarumin aiki na Gyara da rubuta sabbabin Articles.

Da sauran makaloli da su ke bukatar gyara. Kamar sabon Taken Kasar Nigeria da Shugaba Tinubu ya amince da shi..

Domin cigaba da bunkasa wannan Gagarumin aiki na Gyara da rubuta sabbabin Articles.

Da sauran makaloli da su ke bukatar gyara. Kamar sabon Taken Kasar Nigeria da Shugaba Tinubu ya amince da shi..

Domin cigaba da bunkasa wannan Gagarumin aiki na Gyara da rubuta sabbabin Articles.

Da sauran makaloli da su ke bukatar gyara. Kamar sabon Taken Kasar Nigeria da Shugaba Tinubu ya amince da shi..

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na gyara Article na wasanni. Da Kuma Karin gyara kananan Hukumomi na Najeria

Abdoulmerlic[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Wannan data support zai taimaka wurin kara bada himma a edits da kuma gyare-gyare a wikipedia Hausa. Data support zai kara bada kwarin gwiwa wurin yin edits.

Zai taimaka man wurin samun sauqin anfani da yanar gizo domin bada gudummuwa ta a wikipedia.

Sannan a ko wani lokaci edan mutun zai yi abu, ba wai dole sai an dauki wani an ba wa mutun ba kafin yayi abin da zai gina kansa da shi ba, amma duk da hakan bada gudummuwa ko kuma tallafi irin na data support na kara wa mutun motivation wurin yaga ya bada ainufin gudummuwar sa domin ko ba komai an tallafa masa ta hanyar data support.

Nagode sossai.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ahalin ynx ina kan edits da gyare-gyare a sashen hausa na Wikipedia

Bayanin application[gyara masomin]

Domin cigaba da kuma ɓunƙasa gyara da ƙirƙirar muƙalu a Hausa Wikipedia, domin hakan zai ƙaramin ƙwarin gwiwar cigaba da bada gudunmuwa a Hausa Wikipedia fiye da yadda nakeyi, ina fatan kuma zan dace domin cigaba da bunƙasa wannan runbun ilimin, sannan wannan tallafi tabbas yana taimakawa editoci saboda galibin editocin mu marasa ƙarfi ne, bada wannan tallafi zai ƙara azama ga ni kaina dama sauran editocin Hausa Wikipedia.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na ƙirƙiri maƙololi da dama tare da bunƙasa wasu

SaniRabo[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Saboda Data Support da Za'a bani shi zai qarfafa mun gwiwa na cigaba da Bayar da gudummawa ta a shafin Hausa wikimedia. Rashin support din yasa bana samun cikakken lokaci nayi editing a shafin tun bayan bude account dina a shafin. Idan Allah yasa aka bani wannan data support din zai taimaka sosai wurin qaramin qaimi wurin Bayar da gudummawa Mai tarin yawa. Na qirqiri wanna account din nawa tun a shekara 2021 a watan yuni amma bansamu zarafi dana bayar da gudummawa ba sosai ba.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Fassarar mujallu da muhadara

BnHamid[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina mai neman wannan tallafi don zai cike gibin da ni ke samu a wasu lokutan na rashin Data. Rashin Data ka jawo cikasa na wasu lokutan da na samu lokacin ina so in bayar da gudummawata, amman rashin Datar kan haifar da rashin bayar da gudummawata a wannan lokaci. Samun wannan tallafi da gidauniyar Hausa Wikipedia ke bayarwa a gareni, na nufin matsalar tsikon bayar da gudummawata a bangaren cigaban Hausa Wikipedia ya zama Tarihi.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Kasancewa ta Admin a Hausa Wikipedia, hakan na nufin ina da ayyukan da yawa da na ke bayarwa hankali sosai.

Yanzu ina bin diddigin inganci tsofaffi da sabbin Makalolin da aka ƙirƙiro, don gyara su musamman sa ka musu RUKUNI wato CATEGORY hakan zai bamu damar yin aikin tantance su cikin sauri a gaba don gane ingantattun makaloli gami da goge waɗanda basu kai munzalin zama makala ba, ko gyara wadanda su ke bukatar gyara gami da Inganta wadanda ke bukatar ingantawa tare da saka Manazarta.

Bayanin application[gyara masomin]

Saboda na samu karin dama ta tallafi, zan kara himma wajen yin gyaran fuska a shafukan Wikipedia da kuma sauran 'yan uwanta. Ni mace ce da ke da kishin harshen Hausa, kuma na sadaukar da kaina wajen inganta Wikipedia ta Hausa. Wannan tallafi zai zama kwarin gwiwar da nake bukata domin ci gaba da aikin gyara da kuma bunkasa ilimin Hausa a duniyar intanet. Sannan kuma wannan tallafi zai sa ji kamar Nima ina daya daga cikin mamba a gidauniyar Wikimedia.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

A yanzu na mayar da hankali kan kirkirar sababbin makaloli a Hausa Wikipedia da kuma yin gyare-gyare a Wikidata, misalin makaloli da na ƙirƙira a Hausa Wikipedia sune, Ilimi a Misira, Haɗin gwiwar Ilimi Afirka, Karfafawa mata a Najeriya, Haɗin ilmantarwa

Ibrahim Sani Mustapha[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman tallafin data support ne saboda na samu damar da zan bada gudummawa ta a Hausa Wikipedia tare da yan'uwanta,samun wannan tallafin na data support zai karamin ƙwarin guiwa bisa yin himma wajen ci gaba da kirkirar bayanai a cikin shafukan Wikipedia,wikidata, Wiktionary, da ma sauran wiki yan'uwansu tare da yin gyare-gyare acikin kowannen su.Baya ga haka samun wannan tallafin na data support zai sa na kara samun damar rubuta Articles da yawa akowane lokaci a koda yaushe.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na rubuta Articles da dama kamar https://ha.wikipedia.org/wiki/Melvin_Ejim https://ha.wikipedia.org/wiki/Obinna_Ekezie https://ha.wikipedia.org/wiki/Precious_Achiuwa kuma nayi gyare-gyare da yawa

Ashiru Lawal[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman data support ne domin samun sauƙin amfani da yanar gizo wajen bincike tare da wallafa abubuwa masu ma'ana a cikin shafin Wikipedia, saboda Wikipedia wata hanyace da ya kamata mutane su yi amfani da ita wajen watsa ilimi da fasaha tare da ƙara samun ilimi mai amfani. Saboda na ƙara samun damar ziyartar Wikipedia kowane lokaci, saboda Wikipedia wata dama ce da mutane ke da ita da za su shiga su faɗaɗa ilimi da fasaharsu ta intanet.


Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina shiga Wikipedia domin gyare-gyaren wasu abubuwa, da kuma ɗora wasu daban.

Saudarh2[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman data support ne sabo da ze kara mani Karin karfin gwuiwa sosai wajen bada gudun mawo ta a hausa Wikipedia... wajen kirkire kirkiran makala da edit.. zan samu damar yin ammafani da shi wajen shiga shafin Wikipedia a ko da yaushe wajen sa data na bada gudun mawata a hausa Wikipedia.. Zan samu damar shiga na gyara muqalolin da suke da kura kurai a cikin sa sosai.. Da kuma wajen fasaara maqalolin da babu su a hausa Wikipedia.


Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina kokari wajen editin da kuma kirkiran mukalolo daban daban masu ma a na.. na kirkira article da dama akwai article mai dauke da tatsuniyoyin hausa wanda nake kan kirkira tatsuniya daban daban.

Abubakar Yusuf Gusau[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan data support din saboda samun Kwarin gwiwa wajen inganta shafukan Hausa Wikipedia da Wikipedia gaba daya. Dan cigaba da bada ingantaccen gudumuwa Wannda al uman Hausa zasu qaru da shi wajen samun inganttaccen illimi a bisa qa’ida. Da ku jajircewa wajen bincike mai ma’ana wanda na tabbata abun wanda dubban mutane zasu qaru dashi kuma zasuyi aiki dashi a bisa qa’ida. Rashin data yana daya daga cikin abunda ya ke karyamana gwiwa wa gen Edith a Wikipedia.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina edit da kara bayanai da translation a Hausa Wikipedia musamman Hausa Wikiqoute.

Smshika[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Enah neman wanan data support dine sbd nasamu na ƙarin siyan data domin nacigaba da samun ƙwarin guwwama ma bada gudunmawa a Hausa Wikipedia da sauran wasun aikace-aikace na gidaniyar Wikipedia, koma still wanan data support din ko Internet support za temakamin sosai musaman yanda yanzu data ta ƙara kudin in dae nasamu wanan data support din zanyi farin ciki sosai, koma zancigaba da samun ƙwarin gwiwa koma na zage damtsi domin cigaba da bada gudunmawa na ba dare babu rana

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na bada gudunmawa sosai a hausa Wikipedia koma kulin inacin badawa

fateekachan[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman data support dinnan ne Saboda Zai taimaka min sosai wajen ganin na bada gudunmawar da ya kamata a wikipedia...,.....Saboda Zai taimaka min sosai wajen na bada gudunmawar da ya kamata a wikipedia hausa dama wikipedia foundation dafatan Allah yasa inada rabon samu Domin cigaba da bada gudunmawar da yafi Wanda nake bayarwa a da nagode Allah ya Taimake mu yabamu ikon cin ma manufar mu na ganin an bunqasa gidauniyar wikipedia.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

editing,da rubuta mukala

Bayanin application[gyara masomin]

Saboda yana taimakawa sosai wajen siyan data kuma mutum zai kwana biyu yana bada gudummawa batareda wani matsala ba kuma yana kara wa editoci karfin gwiwa sosai. sannan kuma gaskiya akwai actives user wanda suna aiki sosai kuma basa samun tallafi tako ta ina dan haka a ganina suya kamata a dinga bamawa tallafin data support akwai wayen da sai sufi karfin watanni basuyi komai ba kuma sai kaga sunan su a cikin wayan da za’a ba data support Allah ya taimake mu AMEEN

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ah gaskiya ah ko wani wata inayin translating articles sama da 20-50 Wanda baxan iya cewa ga iya abinda nayi ba

Ustaxabunuhu[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan tallafin na data support daga hausa Wikimedia ne domin in samu isashshiyar damar Kara hazaka wajan yawan kirkira da gyaran mukaloli a hausa Wikimedia, domin ba ko wane lokaci ne Nike samun damar gyara ko kirkira mukaloli ba saboda wani lokacin su in wayi gari Banda isheshshen data da zan samu damar yin editing. A dalilin haka be Nike bukatar wannan tallafi da hausa Wikimedia take badawa na data support.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Na kirkiri wasu mukaloli kamar abinda ya shafi wasu garuruwa dake kasar Panama da kuma mukalolin wasu mashuhuren mutane kamar mawaka da sauran su.

Umar A Muhammad[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

1 Ina neman data support ne saboda in kara himma da kokari wajen yin aiki sosai a Wikipedia da inganta Wikipedia ta harshen hausa da Kara fahimtar da mutane su San me ake nufi da Wikipedia 2 Data support na Wikipedia Yana Kara Mana kara Mana himma waje gyara mukala 3 Data support ya Sanya mu ji kamar Koda yaushe ana ganin abun da mukeyi Kuma ganin haka Yasa da mukara kwazo dun muzama kwararru. Data support Yana matukar tai maka Mana musamman ma Yana yin yanda ake ciki na tashin tattalin arziki nakasa, Wikipedia da Wannan data support din ne kesa asa min daman yin jawabi Mai gamsar wa a harka na gyare gyare a Wikipedia, Ina farin ciki inga Ina gyare gyare Mai gamsar wa tare fahimtar wa, hade da ilmar tar wa a Wikipedia

Wikipedia tamune a yau da kullum Wikipedia Koda yaushe tana Kara sabuta rayuwan mutane duk ta sanidiyan Wikipedia data support


Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

1 Alhamdulillah article ne Wanda yake bayani game da godema Allah 2 yanayin tashin Duniya tana bayanine game da karshe duniya

Naja'atu Bintoo Usman[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Dalilina da yasa nayi applying grand din Data support saboda ina so in bada gudunmuna kullum a hausa Wikipedia pages. Kuma dama Data ce matsalata Ina so in na samu in Dunga ba nima tawa gudunmuwar a ko wacce rana. Da Kuma idan na samu data support zan fi samun kwarin gwiwan yin gyaran rubutu,kirkiran articles , applying grand da sauran su. Kuma ko ban samu ba zan bada gudunmuna ta sabowa in inganta yaren Uwa ta Hausa. Nagode

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina editing

Jalamcy2023[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina Neman taimakon data support ne don ya taimakamun wajen cigaba da aikina na Wikipedia sannan zansamu damar fada da aikina sosai idan nasamu taimakon data support hakika zanyi farinciki sosai sannan zan dage da wallafa shafuka da dama da uploading in abubuwa dayawa Dan last da aka bayar bansamuba Amma naci GABA da aikina Amma taimakon zaisa mukara dagewa sosai sannan zamu himmatu akan aikin mu har mukoyar da wasu nagode

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Nayi aiki a wiki common sosai da Wikipedia

To shikenan[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Domin taimakawa wajen inganta wikipedia DA ayyuka masu yawa,Wikipedia sun kaddamar DA gasa DA kuma program masu yawa a wannan shekarar,kssancewa duk Ina cikiin masu bada gudumuwa,hakan zai taimakamin wajen himma DA kuma rashin samun tsaiko wajen kaddamar DA ayyuka masu yawa kuma cikin natsuwa,Wikipedia zasuje taron karawa juna sani a Abuja halartar taron yana bukatar ayyuka DA yawa,nakasance wanni lokacin bana samun damar yi saboda rashin wasu abubwan DA ake bukata

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ni edita Ne, Wanda yakirkiri mukala DA dama,kamar mukalar yan kwallo trossard,jakop kiwor ,William saliba da sauransu

Abubakar Yusuf Gusau[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannnan data support din ne dan inganta shafukan Hausa Wikipedia da sauran shafukan wa inda suka daganci Wikipedia gaba daya. Wannan shi zai bamu kwarin gwiwa wajen jajer cewa wajen bada gudun mawa mai anfani da inganci. Rashin data yana daya daga cikin abun da yake bamu rauni wajen editing shafukan Wikipedia musamman mu Hausa community wanda muke facing bara zana na rashin tallafi na data.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina editing a Hausa Wikipedia da Kuma translation musamman a Hausa Wikiqoute dake incubator.

Khalifah[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan data support din domin zai taimaka min wajan yin edits da yawa sannan hakan zai taimaka man wajan kirkirar sababbin mukaloli masu ma’ana. Sannan kuma idan na samu wannan tallafin zai taimaka min wajan yin edit cikin nutsuwa ba tare da fargabar karewar data ba. Kuma hakan zai taimakeni in dinga Jin kwarin gwuiwar yin edits sosai kuma edit mai ma’ana . Data support zai taimaka man wajan yin aiki mai kyau.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Karatu da kuma edits

Umar-askira[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman data support ne Domin cigaba da gudanar da editing a Hausa Wikipedia a karkashin Hausa Wikimedians User Group wanda aka saba ko wane wata. Sannan fassara makaloli da babu su a hausa Wikipedia sannan inganta makaloli a da sanya hotuna a commons. A halin yanzu na mayarda mafi yawan kason gdunmua na Fassara da mediawiki dukdashima din fassara nafi gudanar na shafi. Wannan tallafin internet data zai kara min kwarin gwuiwa wajen gudanar da editing a Hausa Wikipedia.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Fassara makalai da kara hotuna a commons da sanya bayanai a wikidata sannan ina bada gudunmowa a mediawiki

M I Idrees[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Gaskiya Ina neman wannan tallafin ne don samun damar cigaba da wasu ayyuka masu matukar muhimmanci na Wikipedia, domin yana matukar taimakawa wurin Sanya mutun ya doge kuma ya jajirce ganin cewa ya cigaba da bayarda gudunmawa ba dare ba rana. Kuma ina fatan za'a duba wadannan dalilai kuma abani wannan tallafin mai tarin albarka. Gaskiya Ina neman wannan tallafin ne don samun damar cigaba da wasu ayyuka masu matukar muhimmanci na Wikipedia, domin yana matukar taimakawa wurin Sanya mutun ya doge kuma ya jajirce ganin cewa ya cigaba da bayarda gudunmawa ba dare ba rana. Kuma ina fatan za'a duba wadannan dalilai kuma abani wannan tallafin mai tarin albarka.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Kirkira da gyaran wasu makalai

Ablaffuntua[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Muna son wanan data support domin mu qara Samun qarfin guwa don Bada gudun muwa ta habbaka rubutun yaran Hausa aduniya. Dolle su mutum yana da qarfin ta hanyar mallakar kayan rubuta da karatu na zamani din yin rubuta me ma'ana da fa'ida so sai, Don haka Dolle se mun. Samu gudun muwa don yin aikin da Kyau babu qaqautawa, Shi yasa nike fatan Samun tallafi daga wanan gidauniya me albarka da dun bin tarihi aduniya

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina nan de Ina ta nazari article da zan yi rubuta akan sa.

Habibah A Jisambo[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Dalili shine saboda na Bada gudun hi da abubuwan da dama wajen yin wanan tafiya especially gurin yin editing innajin dadin haka saboda akwai abubuwan karuwa dalilin hakan nakaru da a.bubuwan da dama inna lafahari da hakan wani abun bansan Shiba ammah dalilin editing nakaru da abubuwan da dama alhamdulillah inna farinciki da hakan hakan yakara bani kwarin gwuwa sosai akan wanan aiki inna Mai alfahqri da wanan ayuka sekuma taro daàkeyi Shima anakaruwa dashi sosai wasu sunzo daga Abuja kaduna zaria hakan abun Jin dadine ana karuwa da juna sosai

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Editing

Abdulrahman tahir shika[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina bukatan data support na wikipedia sabida in kara Himma da kokari sosai wajen kara ma mutane Ilimi akan wikipedia nima inzama mai kara ilimi a wikipedia da wayewa sama da Wanda nakeda da shi ada nadade inaji anacewa wikipedia tana bada data support Amman ni bantaba samuba, data support zaisa ni da nakusa dani dama Wanda yasan ina harka na wikipedia social media yasa shima yace in bode masa sabida yasan shima watarana zai samu wannan taimako da wikipedia take badawa na data support WIKIPEDIA TAMUNE NAYAU DA KULLUN MUNA TARE DA WIKIPEDIA KODA YAUSHE WIKIPEDIA ALHERI GA AL UMMA DUNIYA BAKI DAYA

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

nayi gyara sosai akan wata mukala mai suna Karamar Hukumar Giwa ita dai karamar hukumar Giwa dayane daga cikin hukumomi na kaduna Wanda akeda tana da babban kasuwa Wanda akecinta rana alhamis da lahadi

Mansir Yusuf[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan tallafi ne na data domin na cigaba da gyara a Wikipedia, na a baya na nemi wannan tallafin kusan koro biyu amman ban taba samu ba, ina fatan wannan karon na samu, rashin data yakan hanani editing a wani lokaci dan haka wannan tallafi na data nasan zai taimaka min sosai wajen ganin na cigaba da gyara a shafin Wikipedia, sannan ina fatan a wannan karon na samu tallafin saboda inaso naga na kware a gyara a Wikipedia

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Gyaran makala

Legendry3920[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman tallafin data ne saboda samun sauqi da rangwame wajen sayen data domin ingantawa da gyara muqalloli a hausa wikipedia da kuma ma sauran projects din wikimedia foundation, sannan shirin data support yana kara karfafawa editoci gwiwa wajen ci gaba da jajurcewa ta hanyar bada cikakkiyar gudunmuwa a hausa wikimedia, domin burin ko wane cikakken edita yana so ya ka sance zaqaquri wajen yada ingantaccen ilimi a duniya.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

A kwanan nan na kirkira kuma na inganta articles da dama Kamar irinsu shafin (Denis Súarez, Olakunle Oluomo, Maryam Uwais, Titus Uba, Oshodi Tapa, Uche Ugwu, Charles Udoh. Da dai sauransu).

Abdull kwasha[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Dalin dayasa nike neman tallafin saboda insamu sauqi gurin yin edit kuma hakan zai taimaka man wajen kirkirar sababbib maqaloli da kuma yin gyare gyare masu ma'ana yanda mainkaratu zai fahimta da kyau. Sannan hakan zai taimaka man wajan kirkirar sababbin mukaloli masu yawa kuma masu ma'ana. Kuma samun wannan tallafin zai sa inyi gyara ko kuma in kirkiri mukala ba tare da fargabar karewar data ba ko wani abun.

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Gyara da kuma kirkirar mukala

Hauwa'u lawal ardo[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wanna data support dine saboda nasamu na karin siyan data domin nacigaba da samun kwari guwwama ma bada gudunmuwa a Hausa Wikipedia da sauran wasu aikace-aikace na gidauniyar Wikipedia,kuma still wanna data support din ko internet support zai taimakamin sosai musaman yanda yanzu data ta kara kudi,indai nasamu wanna data support din zanyi farinciki sosai,kuma zanchigaba da samu kwarin gwiwa kuma na zage damtsi domin cigaba da bada gudunmuwa na ba dare ba rana nagode

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Nabada gudunmuwata daidai gwargwadon domin nayi editing a Wikipedia,waki common and wakidata koma haryanzu Ina chigaba da bada gudunmuwar ta

Abdulmuddalib labrahim Salisu[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

ni dai ina neman wannan tallafi ne domin na bunkasa gyara da nakeyi a wikipedia ganin ina da karamin karfi ba koda yaushe nake sanya data ba hakan ina da tabbacin zai taimaka min wajen ninka gyaran da nake a shafukan wikipedia hakika ina bukatar wanna tallafi na data kuma wannan ba shi ne karo na farko dana fara neman wannan tallafi ba amman ina fatan daga wannan karon na cigaba da dacewa da samun wannan tallafin domin cigaba da gyara a wikipedia

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

gyara

Abubakar Kaddi[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Tallafin data da nake nema ina da tabbacin zai taimaka min wajen kara gyara da kirkirar makala a Hausa wikipedia, hakika ina neman wannan tallafi ne domin cigaba da gyara a shafukan Hausa na wikipedia, tabbas wannan abun farin ciki ne samun irin wannan tallafi musamman a wannan yanayi kuma zai taimakawa editici Irina sabbi masu San bunkasa ilimi da kuma tunanin mu akan Wikipedia dan haka ina fatan samun wannan tallafi domin zai taimaka min sosai kuma zanji dadin shi idan Allah yasa na same shi

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Gyara da kirkirar makala

Bayanin application[gyara masomin]

Eh Gaskiya data support yana taimaka mana sosai wajen yin contribution a wikipedia saboda wani lokaci bakada kudin siyan data kuma kanaso kayi contributing a wikipedia toh wani lokaci kudin data support sai ya mana kusan wata 2-3 muna siyan data saboda bamu samun tallafi tako ta ina saide wannan tallafin data da ake bayar wa sannan mu mata muna so a kara duba lamariin mata a hausa wikipedia Allah ya taimake mu Ameeen Allah ya kara daukaka Hausa wikipedia Ameeen

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Ina ghere ghere sosai a koda yaushe

Hamza DK[gyara masomin]

Bayanin application[gyara masomin]

Ina neman wannan tallafi ne na data domin na cigaba da gyara a Wikipedia, na a baya na nemi wannan tallafin wata tara kenan da aka bani amma bayan haka duk lokacin da na nema bana samu harma na hakura da neman, kuma wannan support ɗin na kara min kwarin gwiwa wajen yin editing a wani , sannan ina fatan a wannan karon na samu tallafin saboda inaso naga na cigaba da gyara a Wikipedia da sauran yan uwan wiki. NAGODE

Wace gudummuwa kuke ba Hausa Wikipedia?[gyara masomin]

Turai Yar'Adu, Fatima Ibrahim Shema, Saratu Mahmud Shinkafi.