Jump to content

Tattaunawar user:Smshika

Page contents not supported in other languages.
Sabon sashe
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Barka da zuwa!

[gyara masomin]
Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, Sadammuhammad11234! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma ina fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial, ko kuma ka tambayeni a shafina na tattaunawa. Na gode.Em-mustapha talk 15:58, 11 Satumba 2021 (UTC)Reply

Hatsarin dumamar yanayi

[gyara masomin]

Asalam @Sadammuhammad11234, da fatan kana lafiya. Wannan mukalar Hatsarin dumamar yanayi tana dauke da gyrarraki da dama ta yadda ba a iya fahimtar ta yadda ya dace. Saboda haka tana bukatan a inganta ta matuka. Musamman tunda kai ka fassara ta ya kamata ace ka kwatanta ta da ainihin mukalar ta Turanci. Zamuyi mata alamar gogewa sannan zuwa wani dan lokaci idan ba'a gyara ba zamu goge shafin. Nagode

Patroller>> 08:00, 14 Satumba 2023 (UTC)Reply

wslm, nagode, sosai admin zanyi kokari na kara ingatata daidai yanda zan eya Sadammuhammad11234 (talk) 10:11, 14 Satumba 2023 (UTC)Reply

Lura da Fassara (Musamman na taken mukalai)

[gyara masomin]

Aslm @Sadammuhammad11234.. Dan AlLah a rika lura da take (title) na shafuka ta yadda zasu bada ma'ana. Taken wannan shafin Yanayin yanayin duniya wanda a Turance Global surface temperature ba yi ba - Yanayin bisashe na Duniya ko Yanayin wurare na duniya... Patroller>> 08:18, 14 Satumba 2023 (UTC)Reply

Wslm admin enah godeya zan dinga lura daedae gwargwadon yanda zan eya Sadammuhammad11234 (talk) 10:13, 14 Satumba 2023 (UTC)Reply

saka bayanai akan mukalar "Monty Noble"

[gyara masomin]

@Sadammuhammad11234, barka da safiya.. naga kaine ka kirkira mukalar Monty Noble, amma baka rubuta komai acikinta ba, yakamata mu ringa kokarin inganta ayyukanmu.Saifullahi AS (talk) 05:29, 17 Nuwamba, 2023 (UTC)Reply

Neman Qarin Bayani

[gyara masomin]

Assalamu alaykum @Smshika. Naga ka goge mini edits nawa dana yi a shafin Kudancin Ostiraliya, wanda bansan dalilin yin hakan ba. Da nayi nisa da yin edits din, amma yanzun ka mayar mini dashi farko. Don Allah ko zan iya sanin wannan dalilin ko kuskure kayi? @Uncle Bash007 na gode da saka templates da kayi. Amma kuma bansan ko kasan dalili undoing na edits na da @Smshika yayi ba.

Nagode.

Yahuzaishat (talk) 06:18, 4 ga Janairu, 2024 (UTC)Reply

Wa`alaikumu salam @Yahuzaishat ni ba admin ba tayaya zan gogema muƙalanka, ? Smshika (talk) 07:27, 4 ga Janairu, 2024 (UTC)Reply
Just seeing this. Hope you have sorted the issue. Share the page so that I can confirm the issue.
best Patroller>> 12:54, 17 ga Afirilu, 2024 (UTC)Reply

Gogewa

[gyara masomin]

Barka da aiki @Smshika, naga kana ƙirƙirar maƙaloli na Disambiguation wanda ba maƙalolin Wikipedia ne ba. Su wadannan mahaɗu ne da suka haɗa Shafukan Wikipedia masu kamceceniya da suna ɗaya. Duba ƙarin bayani a Nan. Ka sani ana kirkirar irin wadannan shafukan ne kaɗai idan ya kasance akwai shafukan Wikipedia masu kamceceniyar suna. Sabo da haka zan goge dukkan shafukan mahaɗa wato Disambiguation Page da ka ƙirƙira ba bisa ka'ida ba. Nagode Gwanki(Yi Min Magana) 10:09, 23 ga Faburairu, 2024 (UTC)Reply

Gyara

[gyara masomin]

Aslm, @Smshika, muna jin dadin irin gudunmawar da ka ke bayarwa, sai dai wani hanzari ba gudu ba makalolin ka na bukatar Gyara sosai. Ya kamata mu riƙa inganta duk makalar da muka fassara ko kirkira sannan ba ka saka masu Manazarta wanda hakan shima ya dace a saka, kasancewar idan aka fassara makala kusan Manazarta copying kawai za ayi daga inda aka fassarota ba wai sai an sha wahalar neman madogara ba.

Na bi ayyukan ka a tsanake kuma lallai akwai bukatar ka inganta aikin ka musamman irin rukunin aikin ka na fannin Yaruka da ka ke fassarawa na da raunin da suke buƙatar gyara matuka (kasancewar makalar da ta shafi yare/harshe na da SARƘAƘIYA KWARAI, la'akari da wasu kalmomi bamu da su a Hausa ko da akwai lallai suna da wahalar juyawa idan kuma mun juya su ɗin a Hausa to fa marasa zurfin tunani ba lallai su fahimci mi ake nufi ba) don fahimtar mi ake nufi. BnHamid (talk) 08:50, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply

Nagode sosai da gyran da kayinmin yallabai @BnHamid ammah wadanan muƙalolin da na ƙirƙira na yaruku sun woce wata biyu da na ƙirƙire su sbd lokacin munayin wata gasar ne koma a lokacin @Gwanki yayinmin magana na gyra yanzu yau na ƙirƙira wasu ko kaga kuskure a cikinsu? Smshika (talk) 09:20, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
Manufar duk wata GASA shine a kawo cigaba bawai don kawai a faranta ran waɗanda suka samu nasarar lashe gasar ba. Hakan na nufin bai kamata mu mance da muhimmanci wannan farfajiya ba (abin nufi anan kar burin samun rabo a gasar da muke yi, ya saka mu yi wa Hausa Wikipedia illa, ta hanyar yin gyara ko fassara walau mai kyau ko akasi, wanda kan kawo ci baya idan akasi aka samu). Koma tunda an gama gasar ya dace a bi diddigi don taskance su, kasancewa makalolin da aka wallafa anan, na nan don anfanar Al'umma na din-din-din...
Rashin gyara su illa ce, ya fi kyautuwa mu gyara makalolin da aka riga aka fassara fiye da mu kirkiro sabbi, don kaucewa masu nazari su fahimci abin ba daidai ba wanda hakan illa ce garemu bayan su masu nazarin a wannan kundi. BnHamid (talk) 09:52, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply

Eh

[gyara masomin]

Eh Akwai gyara ga wasu da ka ƙirƙiro misali WANNAN MAKALAR ta na bukatar gyara kafin a iya fahimtar mi ake nufi. Kuma baza ka haɗa ta da ƴar'uwarta ta Turanci wanda daga nan ka fassaro ta wurin inganci karantawa da Ma'ana ba.

Akwai f'ida makala ta yi gogayya wurin inganci da kusan kashi 80+ bisa 100% daga kishiyarta da aka fassarota daga can duba da fassara ce akayi ba wai sabuwar makala bace. Sannan bin ka'idojin Rubutun Hausa na da amfani. Da fatan zamu gyara. Na gode. BnHamid (talk) 10:03, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply

tom nagode Smshika (talk) 11:14, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
@BnHamidNagode da tunasarwa, kuma a koda yaushe ina ƙoƙarin ganin na bunƙasa maƙalolin Hausa Wikipedia, ganin Wikipedia encyclopaedia ce wacce ta baiwa kowa damar gyara to inaga idan nayi wata maƙala ba dai-dai ba zaka iya gyarawa batare daka tuntuɓe ni ba, saboda shi ilimi kogi ne ba komai ne zan iya sani ba, sannan kaima idan kayi gyara a wata maƙala dana ƙirƙira ka taimaka wajen bunƙasa ta, nagode. Smshika (talk) 12:59, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
Eh hakane ta ba ka dama haka-zalika dokar Wikipedia ta yarje a yi gyara musamman gyaran ma kai ne silar sa, kuma nima zan iya gyara ta. Amman cigaba da kirkiro wata ba ka gyara wadda ka ƙirƙiro ba, mike amfanin hakan ? Ko sai gyaran ya kai inda tsirarun mutane ba za su iya da shi ba ?, ko sauri yin wata makalar zai hana ka gyaran wacce ka fara kirkirowa ?, bayan gyaran ya fi amfani fiye da ƙirƙiro wata makalar.
Ganin kai ka ƙirƙiro ta ya fi kyautuwa ka gyara ta kafin ka yi wata kuma. Hakan zai baka damar kara kwarewa kuma wani editan ma zai kiyaye ki dan ganin an maka gyara akan kuskure rashin hakan kuma zai sa wani ma gobe ya yi. Ɗin haka kin gyara makala kuma ka cigaba da ƙirƙiro wata hakan na nufin wankin hula ya kamu dare. Ya kamata ka kara sani, riga kafi ya fi magani!. BnHamid (talk) 18:05, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
Kuma da kake cewa ta baka dama. Don haka idan na ga gyara kawai inje in yi ba sai na faɗa maka ba. Ai wannan aikin ba sai ka faɗa ba. Sannan ina so ka sani Nima ita ta bani dama idan ana aikata kuskure inje in gargadi mai yi don magance matsalar daga tushen matsalar kafin ta girmama. Kuma a bisa ka'ida na yi maka gyaran, haka-zalika ba kai kadai aka taba cewa wane ya kamata kayi kaza dalili kaza ba. BnHamid (talk) 18:12, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
@Smshika. BnHamid (talk) 19:39, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
To allhmdllh naji duk bayanan ka, abinda zance maka ni dai ina iya bakin ƙoƙari na, inaga ai kai admin ne, to a duk lokacin da kaga wata maƙala wacce nayi wadda bata dace ba ko take da kura-kurai zaka iya goge ta, hakan ma gyara ne kayi wani sai ya sake fassara ta. Nagode Smshika (talk) 19:44, 4 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
@Smshika ya kamata kasan irin maganar da za ka riƙa yi !. Ka je ka bi tarihin kowa, ba wanda ba'a taɓa yi ma gyara ba a shafin tattaunawar sa. Amman kai an maka magana har zaka buɗa baki kace aje a gyara ba sai an maka magana ba. Wannan maganar kuskure ce da ka fade ta, kasancewar muna mu'amala yadda ya dace a wannan wuri, bugu da kari a dokance na ankarar da kai, sannan abinda ya haɗa mu yafi karfin ka buɗa baki ka faɗi irin waccen maganar.
Abu na karshe shine na faɗa maka kuma na sauke hakki. So duk wani abu da kai ba ni zai shafa ba, kasancewar akwai dokar ta za tai aiki. BnHamid (talk) 11:41, 5 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply
Masha Allah, nagode sosai da shawara, kuma zan cigaba da iya irin ƙoƙarin da zan iya na bunƙasa Wikipedia, Nagode. Smshika (talk) 14:44, 5 ga Yuli, 2024 (UTC)Reply

Translation request

[gyara masomin]

Hello, Smshika.

Can you translate and upload the article about the prominent Turkish economist en:Dani Rodrik in Hausa Wikipedia?

Kindest regards, Moroike (talk) 10:38, 24 Disamba 2024 (UTC)Reply

HI moroike
i wiil do it Smshika (talk) 13:16, 24 Disamba 2024 (UTC)Reply
Thank you. Moroike (talk) 13:48, 24 Disamba 2024 (UTC)Reply
I've done the translatiom. I really appreciats Smshika (talk) 14:01, 24 Disamba 2024 (UTC)Reply
Thank you very much for the new article and I wish you a Happy New Year. Moroike (talk) 14:06, 24 Disamba 2024 (UTC)Reply
Thank you sir Smshika (talk) 14:13, 24 Disamba 2024 (UTC)Reply

Thank you for being a medical contributors!

[gyara masomin]
The 2024 Cure Award
In 2024 you were one of the top medical editors in your language. Thank you from Wiki Project Med for helping bring free, complete, accurate, up-to-date health information to the public. We really appreciate you and the vital work you do!

Wiki Project Med Foundation is a thematic organization whose mission is to improve our health content. Consider joining for 2025, there are no associated costs.

Additionally one of our primary efforts revolves around translating health content. We invite you to try our new workflow if you have not already. Our dashboard automatically collects statistics of your efforts and we are working on tools to automatically improve formating.

Thanks again :-) -- Doc James along with the rest of the team at Wiki Project Med Foundation 06:23, 26 ga Janairu, 2025 (UTC)Reply

Lura don Inganta Aikinmu

[gyara masomin]

Barka @Smshika, sannu da kokari. Gudummawar ku ne silar kai Hausa Wikipedia inda ta ke a yau..

Duk-da haka, mu riƙa bayar da gudummawa mai kyau, ta hanayar inganta makalolin da mu ka ƙirƙiro, ingancin gudummawarmu shine martabar Hausa Wikipedia da zai ba ta damar yin gogayya da takwarorinta.

Makalolin da ka fassara yan kwanakin nan, na buƙatar gyara, kasancewar makalar da ta danganci Harshe ko Yare na da sarkakiya.., dalilin rasa wasu kalmomin a Yaren mu na Hausa, ko da akwai kalmomin a Hausa to yiwuwar juya su, na buƙata mayar da hankali sosai don ma'anar ta fito yadda za'a karanta har ma a fahimta. Fatan za mu gyara. BnHamid (talk) 16:02, 27 ga Faburairu, 2025 (UTC)Reply

barka da wanan lokacin @BnHamid in sha Allah zan gyra koma in sha Allah da ga yanzu zandiga lura da kyau nagode sosai Smshika (talk) 16:07, 27 ga Faburairu, 2025 (UTC)Reply

Jawo hankali

[gyara masomin]

Barka da aiki @Smshika sannu da kokari da fatan zaka ci gaba da bada gudummawa kamar yadda ka saba. Sai dai ina mai jawo hankalinka game da mukaloli na mata da kake kirkira akan rashin canza identity na wanda ake mukalar akanta. Misali idan mace na yin waka ana kiranta "mawakiya" ba "mawaki" ba sai wurin "ita" wani bin saika sanya "shi". Daga karshe ina maka fatan nasara da fatan cigaban Wikipedia. Pharouqenr (talk) 17:28, 2 ga Maris, 2025 (UTC)Reply

nagode da gyranka @Pharouqenr zan gyra in sha allah Smshika (talk) 17:33, 2 ga Maris, 2025 (UTC)Reply

Saka suna cikin jerin Admins

[gyara masomin]

Barka @Smshika sannu da kokari, a matsayinka na Admin ka garzaya domin saka sunanka Anan Wajan

Pharouqenr (talk) 06:17, 23 ga Yuli, 2025 (UTC)Reply

Ƙorafi

[gyara masomin]

Assalam @Smshika barka da Aiki. Naga ka goge man muƙala mai taken "Ernestine Eckstein" ko zan iya Sanin dalili? A iya sanina kamata yayi kaman magana in gyara idan tana da kuskure ba ka gogeta kai tsaye ba. Ya kamata mu dinga yima juna adalci domin cigaban Wikipedia. Nassmart1 (talk) 06:23, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply

Wa'alaikumu salam malam Nassmart1 muƙalan mai suna Ernestine Eckstein akwai gyre gare da yawa acikinta koma muƙalan bata da ma'ana ko kadan tom a matsayin na, na admin in muƙala bata da ma'ana koma bazata gyru cikin sauqi ba gogeta shiene aikinmu, Smshika (talk) 07:04, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Idan kai wajanka abune mai wahala, mai yiyuwa ni ya zama mai sauƙi a wajena! Saboda haka a matsayika na Admin mai son gyara a Wikipedia gargaɗi shine farko domin ankarar da mai rubutu yasan halin da yake ciki. Nassmart1 (talk) 07:11, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
muƙalan da mukaga zata gyru cikin sauqi etace muke ma,mutum magana, Wani editor ma inmukaga ya zow baya Wikipedia blocking din shie kawai mukeyi ba sai munyin masa magana ba Smshika (talk) 07:22, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Malam kana ƙokari sosai Nassmart1 amma ko yanzu mukalolin da ka ƙirkira da safen nan akwai gyre gyre acikinsu kaman wanan Tafiyar Indiya ta Lindsay Lohan kaga wanan muƙalan zan eya gyrata in nasamu lokacin, tom kaga muƙala yanzu mai karatu ya zow tin a sakin layin farko zai rikice film din a wani ƙasa akayi shie Birtaniya ko Indiya ko America Ni shawaran da zanbaka kadinga karanta muƙala kafin ka wallafa ta Smshika (talk) 07:16, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
@Smshika cikin girmamawa ka dinga tsayawa kana fahimtar rubutu kafin ka yanke hukunci. Lindsay Lohan's Indian Journey shine taken fim din. Domin tabbatar wa ga paragraph din farko "Lindsay Lohan's Indian Journey, fim ne na Burtaniya na 2010 wanda Maninderpal Sahota ya shirya kuma ya samar. 'Yar wasan kwaikwayo ta Amurka Lindsay Lohan ce ta gabatar da shi kuma ta ba da labari. A cikin shirin na tsawon sa'a, Lohan yana magana da wadanda ke fama da fataucin mutane a Delhi, Kolkata da kuma wani kauye a West Bengal. Ta kuma yi magana da tsohon mai fataucin mutane, iyayen yara masu fataucin kaya kuma ta ziyarci gidan mata da yara na Sanlaap a Kolkata. An yi fim din ne a Indiya a cikin mako guda a watan Disamba na shekara ta 2009. Lohan ya shiga cikin aikin bayan ya sadu da Sahota a wani taron zamantakewa kuma ya nuna sha'awar shiga."
Wannan shine paragraph na farko, sannan Taken fim din shine "Lindsay Lohan's Indian Journey" fim din anyi shi a Burtaniya. Saboda haka babu abin rikicewa a cikin wannan paragraph din.
Daga karshe, hallau a cikin girmamawa sir, a matsayin ka na facilitator na human right kada matsayin ka na admin yasa ka zaɓi ɓangare. Nagode sosai fatan zamu samu fahimtar juna. Nassmart1 (talk) 07:27, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Ikon Allah yanzu kana zargina na gogema muƙala ne sbd kar kaci gasar wiki for Human rights? Smshika (talk) 07:31, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Nassmart1 nima Da ga ƙarshie duk yanda zaka dauke ni ka daukeni Allah yasan zuciyana koma indae kacigaba da ƙirkiran mukalolin marasa ƙyau zaiyi delete dinsu koma inkagi dainawa zan dau mataki Shariya Wikipedia yanda ta tsara. Smshika (talk) 07:37, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Ranka ya dade @Smshika akwai matakai da yawa na rufe mutum, amma ka sani kamar yadda sauran masu gasar suke amfani da Content translator haka nakeyi! Kuma kafin wallafawa ina bin ƙa'ida sosai. Saboda haka nagode da gyaranka. Mu kwana lfy Nassmart1 (talk) 07:47, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Nassmart1 Ni wlhy bana nufika da wani abu wlhy sai Alkairi amma kai kuma ka change abun zuwa wani abu ka nunamin kamar banson kaci gasar wiki for Human rights ne ko? Aa wlhy tin da akafara Gasar bai wuce sau daya ba na shiega Dashboard din gasar koma wlhy Bansa ma kana participant ba, Smshika (talk) 07:52, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Nagode da fahimtar juna @Smshika Allah ya taimaka mana baki daya domin kawo cigaba a Wikipedia. A matsayinka na Admin wannan shine aikinka na kula da abubuwan dake wakana. Nassmart1 (talk) 07:56, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply
Aimee Thurman Aimee oga Nassmart1 nagode Smshika (talk) 07:57, 6 ga Augusta, 2025 (UTC)Reply

Notice of expiration of your sysop right

[gyara masomin]
Hi, as part of Global reminder bot, this is an automated reminder to let you know that your permission "sysop" (Admins) will expire on 2026-01-03 09:44:25. Please renew this right if you would like to continue using it. In other languages: click here Leaderbot (talk) 19:45, 28 Disamba 2025 (UTC)Reply