Jump to content

Tattaunawar user:M I Idrees

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Barka da zuwa!

[gyara masomin]
Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, M I Idrees! Mun ji daɗin gudummuwarka. Kuma ina fatan zaka tsaya ka ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimake ka ka fahimci Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial, ko kuma ka tambayeni a shafina na tattaunawa. Na gode. Em-em talk 09:52, 16 ga Maris, 2021 (UTC)[Mai da]

Gasar WPWP

[gyara masomin]

Assalam! Barka da ƙoƙari, ina mai yabawa da ƙoƙarin ku a gasar WPWP na sanya hotuna a shafukan Wikipedia, sai dai wani hanzari ba gudu ba, naga kuna jera hotuna a shafi ɗaya, wani lokacin har hotunan kanfi rubutun shafin yawa. Abinda nake son tunatarwa shine, gasar ba wai ana son kawai aga hoto a shafi bane! Sai dai ana son ne ayi amfani da hoto wurin nunawa da yin ƙarin bayani ga mai-karatu ta hanyar hoton da zai gani, domin hakan zai ƙara gamsar da shi, amma misali; naga ka jera hotuna a shafin ɗan kunne da shafin bango duk dai abu ɗaya suke nunawa, wanda yakamata ne aga hoto ɗaya kawai, idan kuma akwai wani nau'inw/slm, sai shima a sanya amma a tabbatar itama nau'in da aka sanya anyi bayani akanta. Gaskiya, bai dace ba a jera hotuna iri ɗaya a shafi matuƙar hoto ɗaya zai wadatar da abinda ake so. Dafatan za'a ƙara bibiyan [[m:Wikipedia Pages Wanting Photos for Hausa Community 2021#2|]] dokokin gasa. Nagode. M-Mustapha talk 21:03, 30 ga Yuli, 2021 (UTC)[Mai da]

W/salam naga dukkan bayananka kuma insha Allahu nafahimta kuma zangyara, dukda cewa ni sabon user ne. M I Idrees (talk) 19:47, 31 ga Yuli, 2021 (UTC)[Mai da]

Hadisi na Daya (Majma'ul Bahraini)

[gyara masomin]

Assalam M I Idrees, da fatan kana lafiya. Na ga ka rubuta mukala mai take da ke sama. To tabbas inaga baka fahimci abunda ake yi a wannan shafin na Hausa ba. Da farko dai ana bayani ne musamman akan abubuwa, wuri, fitattun mutane da dai sauransu. Zaka iya rubutu ne kadai misali game da Littafin Majma'ul Bahraini cewa littafi ne mai dauke da Hadisan Manzon Tsira (Alaihissalatu wassalam).. sai ka jero hadisi na daya na magana akan.. hadisi na biyu na magana akan.. har zuwa hadisi na karshe. Saboda haka mun goge wannan shafi. Da fatan zaka tsaya ka gyara kuma ka cigaba da ba da gudummawa wanda ya dace a wannan shafin namu na Hausa.

Bissalam Patroller>> 03:06, 21 Satumba 2022 (UTC)[Mai da]

ina lafiya alhamdulillah, hakan yayi matukar kyau da ka goge, amma ai Yakamata ka bincika waya rubuta wannan shafin Farko, nikawai nayi gyara ne acikin shafin domin naga kuskuren rubutu aciki. M I Idrees (talk) 05:57, 21 Satumba 2022 (UTC)nagode matuƙa da bibiya tareda duba ayyukana dafatan zakabani dama muƙulla alaƙar abota dakai malam Bashir.[Mai da]

mukala:Istihara

[gyara masomin]

Aslm, barka da safiyar juma'a Malam Idrees. Hakika nayi matukar farin ciki kuma ina kara jinjina maka da gudummawa da kake badawa a wannan shafi na Hausa Wikipidya. Tabbas wannan mukala zatayi tasiri sosai ga al'umman musulmi, sai dai akwai hanzari guda biyu:

Na farko dai Wikipidiya ba waje bane na koyarda addini ko yin bayani kan addini, amma idan ya zamana an rubuta mukala ba tare da nuna wani kusanci ko ha'inci ba, za'a iya karbar wannan mukala. ka karanta wannan shafin don karin haske akan Wikipidiya https://en.wikipedia.org/wiki/Wikipedia:What_Wikipedia_is_not

Na biyu kuma shine, mukala ba ta zama tabbatacciya a Wikipedia har sai ta cika wasu dokoki, daga ciki shine ya kasance akwai hujjoji (wato reference) masu karfi da suka tabbatar da bayananta. Saboda haka ya kamata ka sanya hujja da ka samo wadannan bayanai

A dalilin haka, zanyiwa wannan mukala alama na cewa tana bukatar a inganta ta, sannan zan gabatar da muhara a shafin tattunawa na shafin: shin wannan mukala ya kamata ta tsaya ita kadai? idan bata cancanta ba, zamu dauketa mu sanya ta acikin wata mukala (misali zamu iya sanya bayanan istihara acikin shafin Musulunci) ko makamancin hakan.

Da fatan ka fahimci bayanai na, kuma zaka tsaya ka cigaba da bada gudummawa a wannan shafin.Patroller>> 07:24, 11 Nuwamba, 2022 (UTC)[Mai da]

wlksm, nima Nagode da bibiyan ayyukana domin ganin abinda nike gabatarwa a duniyar Wikipedia Alhamdulillah, kasani Wikipedia kaface ta samar da ilimi kowanne iri daban-daban kuma kowanne Addini kake kai ko tsafi ko gunki kake bauta, kanada damar zuwa kabada gudunmawarka ga al'ummar duniya ta tsagin yarenda kakeji. Kasanini wannan maƙala baɓu wani nuna son  Kai ko ha'incin aciki kuma idan kagani ka nuna Insha Allah zangyara  ko kagyar
a.
Sai maganar hujja haƙiƙa nasaka hujja domin kuwa hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne yayi bayanin yadda ake yin "istiharan" kuma nasaka hujja inda kan hadisin kaduba da kyau yana cikin sahihul Bukhari wanda sahabi jabir bin Abdullahi ya ruwaito.
Kuma wannan maƙala kasani baikamata a sakata cikin rukunin musulunci ba domin tanada damar tsayawa da ƙƙafarta saboda muhimmancinta, domin mahimmancita yasa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yake koyar da ita kamar yadda yake koyarda karatun Alkur'ani inji( jabir bin Abdullahi ).
Inhar za'a bar waƙa da Rawa suci gashin kansu (sutsaya da ƙafafuwan su) batareda ansakasu acikin rukunin Al'ada ba to Yakamata abarta itama basai an sakata acikin rukunin Musulunci ba.
Kahuta lafiya
Wassalamu'alaikum. M I Idrees (talk) 06:50, 13 Nuwamba, 2022 (UTC)[Mai da]