Ya’u Umar Gwajo Gwajo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ya’u Umar Gwajo Gwajo
Rayuwa
Haihuwa 1964 (59/60 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Ya’u Umar Gwajo Gwajo (an haifeshi a ranar 8 ga watan August shekara ta 1964) a garin Gwajo Gwajo a karamar hukumar Mai'adua. Dan siyasa ne a Jihar Katsina. Ya rike matsayin Chairman na karamar hukumar Mai'adua tun daga shekara 1999 zuwa 2003, ya sake zama Chairman karo na biyu 2003 zuwa 2007 Daga nan ya zama member na Majalisar Dokoki na Jihar Katsina tun daga Shekara ta 2007 zuwa 2011 kuma shine Kakakin Majalisa daga shekara ta 2007 zuwa 2015.[1][2]

Farkon Rayuwa da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifeshi a ranar 8 ga watan August shekara ta 1964.

Ya fara karatunsa na firamare a Gwajo-Gwajo Primary School Katsina a tsakanin shekarun 1972-1978; sannan ya tafi makarantar sakandare ta gwamnati wato Government Secondary School, Funtua a tsakanin shekarun 1978-1983; sannan ya wuce zuwa kwalejin gwamnatin tarayya wato Federal College of Education, Kano daga shekara ta 2000-2002.[1]

Aiki da siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Gwajo Gwajo yayi aiki a matsayin magatakarda a gidan ruwa na Kaduna/Katsina State Water Board, 1987.

Sannan daga bisani an zaɓe shi matsayin memba a Majalisar Dokoki na Jihar Katsina a daga 1991 zuwa 1993; sannan yazo yayi kansila ba'a ƙarƙashin jam'iyyar ba tsakanin 1996 zuwa 1997; sannan ya riƙe matsayin ciyaman na ƙaramin hukumar Maiodua daga shekara ta 2003 zuwa 2004; ya sake komawa kujerarsa na Chairman na karamar hukumar Maiodua a karo na biyu daga 2004-05; sannan ya riƙe kujerar Chairman na riƙon ƙwarya na kwamitin karamar hukumar Maiodua a shekara ta 2007; sannan daga bisani aka sake zaɓarsa kujerar Majalisar Dokoki ta jiya a shekara ta 2007.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 https://blerf.org/index.php/biography/gwajo-gwajo-hon-alh-yao-umar/
  2. https://www.vanguardngr.com/tag/umar-yau-gwajogwajo/amp/