Yankin Garaɓasa na Lagos

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yankin Garaɓasa na Lagos

Yankin Garaɓasa na Lagos wato Lagos Free Zone ( LFZ ) yanki ne na Kasuwanci kyauta da ke Legas wanda ƙungiyar Tolaram ke haɓakawa.[1] Yankin kyauta yana hade da tashar jiragen ruwa na Lekki Deep Sea kuma ya mamaye fili mai girman kadada 830 a Legas.[2][3][4] Yankin garabasa na Legas yana da nisan kilomita 60 daga gabas da birnin Legas. Hakazalika da sauran yankuna masu zaman kansu, kamfanoni a LFZ na iya siyar da duk kayansu a cikin yankin kwastam na Najeriya ba tare da biyan harajin jiha ko ta tarayya ba kuma sai da lasisin shiga da kaya ko fitarwa ba. Haka kuma za su iya mayar da ribar da suka samu da kuma kasafinsu. Raffles Oil da Insignia Systems, Inc. sune kamfanoni na farko da na biyu da suka zo yankin bi da bi. LFZ tana ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar Legas kuma gwamnatin jihar ta ba da filin ga LFZ.[4][5] An fara shi a shekara ta 2002 da fili mai fadin hekta 215. Daga baya a shekarar 2012, kusan hekta 590 ne gwamnatin jihar ta ba da karin fili. Sai dai kamfanin yankin ciniki na 'yanci na Legas ne ya gudanar da aikin.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Lagos Free Zone to attract additional $5bn investment in 4 years". Businessday NG. 2021-03-23. Retrieved 2022-04-22.
  2. "Lagos Free Zone to boost Nigeria's GDP by 2 percent". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2020-11-24. Retrieved 2022-04-22.
  3. "Lagos Free Zone Company floats N10.5bn corporate infrastructure bonds". Vanguard News. 2021-09-19. Retrieved 2022-04-22.
  4. 4.0 4.1 Mugano, Gift (2021). Special Economic Zones: Economic Development in Africa. Springer Nature. ISBN 978-3-030-82311-5.
  5. Mugano, Gift (2021). Special Economic Zones. doi:10.1007/978-3-030-82311-5. ISBN 978-3-030-82310-8. S2CID 243814353.
  6. "Regional Development and Industrialization". springerprofessional.de. Retrieved 2022-04-22.