Yankin Gabar Tekun Neja na Mallakar Turai (Niger Coast Protectorate) ta kasance wata yankin na mulkin mallakar Birtaniyya dake yankin Oil Rivers (Neja Delta) na Najeriya a yau, wanda aka kafa shi a matsayin Oil Rivers Protectorate a 1884 kuma an tabbatar da ita a taron Berlin na shekara daya bayan kafa ta. An sake masa suna a ranar 12 ga watan Mayun 1893, kuma an haɗa shi da yankunan da aka yi haya na kamfanin Royal Niger Company a ranar 1 ga watan Janairun 1900 don kafa yankin Kudancin Najeriya.
Sarauniya Victoria a kan tambari na kare gabar tekun Niger, 1894