Yar gala gala
Yar gala gala wani nau'in wasa ne da ake yi a kasar Hausa. Wasanni na ɗaya daga cikin abubuwan da suke nishadantar da yara, kuma wasan yar gala-gala na daya daga ciki.
Yadda ake wasan A wasan Yar gala-gala ana zan gidaje ne a saman kasa a kalla guda goma, sannan sai masu wasan su rika tsallakawa, duk Wanda yaci gida baza'a sake saka kafa a gidansa ba. wasan yana da dadin yi.[1]
Yadda ake gudanar da wasan
[gyara sashe | gyara masomin]Zana layuka a kasa akeyi a wannan wasan, sai a raba su gida gida kamar gida 6 ko fiye da haka, yaro zai tsaya daga bakin layin farko ne, sai ya jefa karamin dutse cikin daya daga cikin gidajen, sai ya fara tsalle da kafa daya yana shiga kowani gida har ya kai gidan da dutsen shi ya fada, sai ya dauka abinsa, ya cigaba da tsalle har ya fita daga duka gidajen. Dokan wasan nan shine ba’a so dutsen ka ya dira akan layi, sai dai a cikin gida.[2]