Jump to content

Yaye a ƙasar Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
yaran da ake yayewa

Yaye yana nufin wani mataki ne da idan yaro ya kai shi za'a hanashi shan nono. Wasu suna yaye yaran su daga shekara biyu Abinda yayi ƙasa da haka, amma dai a Musulunci kamar yadda yazo acikin Alqur'ani mai girma[1] yaye shekara biyu ne cikakku, sai dai idan mace mai saurin haihuwa ce to takan yaye ɗanta daga zaran ta sake samun wani cikin.[2] Akan fara koyawa yara cin abinci kafin a janye su daga shan nono, saboda koda babu nonon abinci zasu ci don su rayu.

A al'adance idan aka yaye yaro a ƙasar Hausa akan rabashi da mahaifiyar sa na ɗan wani lokaci kamar sati ɗaya daga nan har wata wani ma shikenan chan za'a barshi gurin ƙanwar mamar sa ko kakarsa ta mace riƙo har girma.

Akan kaiwa ɗan yaye kaji da gara ta abinci da dai sauransu wani lokacin ma kajin da ake tara masa sune za'a tattala masa har su zama dukiya mai yawa, sai dai yanzu zamani ya chanja musamman a birane ba'a kallan wannan al'adar, amma a ƙauye har yanzu sunayi.

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-05-22. Retrieved 2021-05-22.
  2. https://www.bbc.com/hausa/news/2011/11/111104_haifikiyaye_week47