Jump to content

Yusuf Tijani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yusuf Tijani
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Okene/Ogori-Magogo
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2015 -
District: Okene/Ogori-Magogo
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2011 -
District: Okene/Ogori-Magogo
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Yusuf Ahmed Tijani ɗan siyasan Najeriya ne. Ya taɓa zama mamba mai wakiltar mazaɓar Okene/OgoriMagongo a majalisar wakilai. [1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Yusuf Ahmed Tijani a ranar 4 ga watan Mayu 1972 a ƙaramar hukumar Okene, jihar Kogi. Ya yi karatun firamare a Nurul-Islamic Primary School Okene, jihar Kogi a shekarar 1984, sannan ya yi karatun sakandire daga shekarun 1984 zuwa 1990 a ƙaramar hukumar Ohiana, Okene. A shekarar 2009, ya yi digirinsa na farko a fannin harkokin gwamnati a Jami’ar Jihar Kogi Anyigba. Ya wuce Makarantar Tsaro ta Najeriya Kaduna inda ya yi digiri na biyu a fannin magance rikice-rikice kuma ya kammala a 2007. [2]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Tijani ya fara aiki ne a shekara ta 2000 a matsayin Kansila na Unguwan Onyukoko a ƙaramar hukumar Okene, jihar Kogi har zuwa shekarar 2003. Ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Alhaji Idris Ibrahim a matsayin mai ba da shawara na musamman. [2] A zaɓen ‘yan majalisar tarayya na shekarar 2011, Tijani ya gaji Suleiman Kokori Abdul inda ya tsaya takara kuma ya yi nasara a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Okene/Ogori-Magongo. Ya sake tsayawa takara a zaɓukan shekarun 2015 da 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar APC kuma ya ci zaɓe a jere, wanda hakan ya sa ya zama ɗan majalisar wakilai karo na uku. [1] Ya ɗauki nauyin kudirori da dama tare da ƙaddamar da ayyukan da suka shafi ilimi, karfafa tattalin arziki da inganta kiwon lafiya a mazaɓar sa. A matsayin karfafawa, ya rabawa al’ummar mazaɓar sa sama da buhu 500 na taki, domin ƙarawa da inganta aikin noma. [3] Bayan haka, shirin “Season Intervention” da ɗan majalisar ya tsara, wanda ya mayar da hankali kan horarwa da karfafawa manoma da ‘yan kasuwa kusan 200 ne suka amfana daga mazaɓar sa. [4]

  1. 1.0 1.1 "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-18. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 admin (2018-11-09). "Background and Achievements of Tijani Damisa". :: Kogi Reports (in Turanci). Retrieved 2024-12-19. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  3. admin (2018-01-23). "Reps Member Tijani Damisa Distributes Fertilizer to Kogi Farmers". :: Kogi Reports (in Turanci). Retrieved 2024-12-18.
  4. admin (2021-10-26). "Rep Member Tijani Damisa Empowers Farmers, Traders in Okene". :: Kogi Reports (in Turanci). Retrieved 2024-12-18.