Zeritu Kebede
![]() | |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | 19 ga Faburairu, 1984 (42 shekaru) |
| ƙasa | Habasha |
| Sana'a | |
| Sana'a |
mawaƙi, jarumi, marubin wasannin kwaykwayo da singer-songwriter (en) |
| Kayan kida | murya |
Zeritu Kebede (an haife ta 19 ga watan fabrairun 1984) ta kasance mawakiya, mai rubuta waka kuma jarumar fim na kasar Ethiopia. Shahararriya a fagen wakoki zamani na Habasha,wakokin ta sun shafi wakokin rock da wakokin kiristanci.
Farkon Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Zeritu, Kebede[1] a Addis Abeba a ranar 19 Febrerun 1984.[2][3] Mahaifinta Kebede Woldegiorgi, ya kasance mai zanen gidaje, sannan mahaifiyar ta Engida Mitiku, ta kasance mata a gidan mijinta wacce take kasa da shekaru 30 da mijinta.
Zeritu Kebede ta girma a Gullele wani yanki a arewacin Addis Ababa. Ta taso a cikin rayuwa ta tsanani kuma ana rabata da sauran yaran unguwa. Duk da haka, Zeritu ta kwashe mafi yawancin lokutan ta na hutun rani tare da kakannin na wajen uwa, wadanda suke da sakewa da kusanci da makwabtansu. A nan ne Zeritu Kebede take samun lokaci da daman yin wasa da yara daga wasu gidajen masu asalin al'adu daban daban.
A matsayinta na yarinya a gida da yake shiru, Gulele, Zeritu Kebede tana yawan karanta littattafai, tana sauraron tatsuniyoyin kasa wanda 'yan aikin gida ke bata, ta kalla kuma ta buga kwallo da dan uwanta, sannan ta kashe lokutanta a kan bishiya tana kallon tsuntsaye da sauran sassan gari don nidhadi. Amma waka ne yafi dace da ita kuma yafi bata nishadi. Tana duba cikin wakokin mahaifanta sannan tana sauraron dun abinda ta ga ya burge ta. Daga cikin jerin wakokin da iyayenta suka ajiye, na musamman ga mahaifinta sune , Nat King Cole, Kassa Tessema, Mahmud Ahmed da sai saurancu; da kuma jerin mawakan da mahaifiyarta ke ji akwai Tom Jones, Muluken Melesse, da kuma Donna Summer. Tana kuma sauraron kaset inda ta san mawaka irinsu Michael Jackson, Whitney Houston, Celine Dion, Michael Bolton, Boyzone, Tracy Chapman da kuma Bob Marley.
Zeritu Kebede ta halarci makarantar firamare ta Lazarist ta katolika
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Addini
[gyara sashe | gyara masomin]Zeritu ta kasance mabiyar Protestantism. A wani bangaren, ta bayyana cewa ta sake komawa cikin Christian; sai dai sabon wakar da ta saka ya bayyana fitar ta daga Christianity.[4]
Wakoki
[gyara sashe | gyara masomin]Albam na sutudiyo
- Zeritu (2005)
- Artificial (2014)
- Eza Alkerehum (2017)
- Love Love Love (2018)
- Azmari Negn (2018)
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "hawassaonline.com – hawassaonline Resources and Information". www.hawassaonline.com. Archived from the original on 2020-11-16. Retrieved 2025-01-20.
- ↑ Aga, Mark T. "50 of the Best Old & New Amharic Music: Songs and Singers — allaboutETHIO". allaboutethio.com (in Turanci). Retrieved 2021-12-13.
- ↑ "LIST: 25 Most Beautiful Ethiopian Actresses". LISTPH. Retrieved 2021-12-13.
