Jump to content

Zeynab Ilhamy

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zeynab Ilhamy
Rayuwa
Haihuwa Istanbul, 29 Disamba 1859
Mutuwa Kairo, 17 Mayu 1918
Ƴan uwa
Mahaifi Damad Prince Ibrahim Ilhamy Pasha
Mahaifiya Münire Sultan
Sana'a
Sana'a aristocrat (en) Fassara

An haifi Princess Zeynab Ilhamy a ranar 29 ga watan Disamba na shekara ta 1859 a Istanbul . Ita ce diya ta biyu a wajan Lieutenant Janar Prince Ibrahim Ilhami Pasha . da Jeshmi Ahu Qadin (ya mutu shekara ta 1905). Ita ce jikokin Khedive Abbas I da Mahivech Hanim . Tana da 'yan'uwa mata biyu, Princess Emina Ilhamy da Princess Tevhide Ilhamy. A shekara ta 1878, Zeynab ta auri dan uwan mahaifinta Yarima Mahmud Hamdi Pasha ɗan biyar na Isma'il Pasha da Jahan Shah Qadin . Ma'auratan suna da diya daya, wacce ake kira da suna Princess Munira Hamdi, an haife ta a shekara ta 1884. Su biyu sun sake aure a shekara ta 1888.

Zeynab ta mutu a Alkahira a ranar 17 ga watan Mayu shekara ta 1918, kuma an binne shi Hosh al-Basha, Imam al-Shafi'i, Alkahira.

Zeynab da Mahmud Hamdi suna da diya daya:

  • Gimbiya Munira Hamdi (18 ga watan Yulin shekara ta 1884, Alkahira - 18 ga watan Nuwamba shekara ta 1944 - Alkahira), ta auri Mohamed Tawfik Naseem Pasha;