Zinabu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zinabu
Asali
Lokacin bugawa 1987
Ƙasar asali Ghana
Characteristics

Zinabu fim ne na ƙasar Ghana na shekarar 1987 wanda William Akuffo da Richard Quartey suka bada Umarni.[1]

Makirci[gyara sashe | gyara masomin]

Zinabu ta ba da labarin wata mayya da ta koma Kiristanci.

Shiryawa[gyara sashe | gyara masomin]

An ɗauki fim din a shekarar 1985 ta hanyar amfani da kyamarar bidiyo, maimakon kyamarar fim. Bidiyo wani sabon salo ne a lokacin, amma Akuffo ya fahimci fa'idar da faifan bidiyo ke da shi akan fim, saboda fim ɗin celluloid ya fi tsada kuma yana gabatar da ƙalubale wajen rarrabawa. Zinabu shirin ya zama fim ɗin Ghana na farko da aka fara shiryawa na bidiyo.

Samarwa[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin da ake shirya fim din na Zinabu, gwamnatin Ghana ta gabatar da dokar hana faifan bidiyo, a wani yunƙuri na daƙile mummunan tasirin da suke ganin cewa fina-finan Amurka da China marasa lasisi na yin tasiri ga al'adun ƙasar Ghana. An dage wannan haramcin ne a shekarar 1987, saboda aikin Akuffo.

Fim ɗin an fara haska shi a Globe Cinema. An tsara wannan wasan ne don yin koyi da yadda ake nuna fina-finai na yau da kullun: na'urar bidiyo masu sauraro basa iya gani.

Gado[gyara sashe | gyara masomin]

Zinabu ne fim na farkon fasalin bidiyo na ƙasar ta Ghana, wanda ya fara sabon nau'in shirya fina-finai na asali wanda zai girma a farkon shekarun 1990. A cikin 1988, an fitar da fina-finan bidiyo guda biyu, amma wannan ya girma zuwa bakwai a cikin 1991, kuma sama da 50 a 1993. Akuffo kuma ya samar da cigaban shirin Zinabu.[2]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Haynes, Jonathan (2010). "What is to be done? Film studies and Nigerian and Ghanaian videos". In Mahir Saul and Ralph A. Austen (ed.). Viewing African Cinema in the Twenty-First Century: Art Films and the Nollywood Video Revolution. Ohio University Press. pp. 45–47. ISBN 978-0-8214-1931-1.
  2. Ukadike, N. Frank (2003). "Video booms and the manifestations of 'first' cinema in anglophone Africa". In Wimal Dissanayake and Anthony Guneratne (ed.). Rethinking Third Cinema. Routledge. p. 222. ISBN 978-1-134-61323-6.