Jump to content

Ƙauyen Gubana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
gubana

Gubana ƙauye ne da ke cikin ƙaramar hukumar Fune ta jihar yobe a Najeriya.

Gubana ƙauye ne da ke cikin ƙaramar hukumar Fune ta jihar Yobe a Najeriya ya kasance ƙauye ne wanda ya kai shekara dari biyu da ashirin da biyar 225 da kafuwa a wancan lokacin Bazemfila mahaifin sarki bah, ya yi ƙaura daga Mai wala zuwa Mai dala, da aka fi sani da (Gubana) tare da ɗansa a dalilin sarkin Mai wala yana alfahari a kullum babu wani mutum kamarsa ko sama da shi a kauyen Mai wala dole ne kowa ya kasance a karkashinsa irin wadannan kalaman sun yi rauni a zuciyar Bazemfila ya yanke shawarar canza wurin zama, da ya yi hijira daga Mai wala, zuwa Maidala. Maidala abokin Bazemfila ne kuma Bazemfila ya fi Mai dala arziki a kauyen, Bazemfila ya rasu ya bar dansa mai suna bah kafin Bazemfila ya mutu yana rike da sarautar Gubana a matsayin sarki domin shi ne mafi karfin hali kuma attajiri.[1]

Masarautar bah ta fara daga shekara ta alif 1880, zuwa shekara ta alif 1930, sarki, ya yi aure kuma ya haifi ‘ya’yansa tagwaye mace da namiji, an haife su a shekarar ta alif 1891, sunan namijin Yerima Ussaini, Yerima haifaffen Gubana ne, kuma ya karbi Masarautar mahaifinsa daga shekara ta alif 1930, zuwa shekara ta alif 1970. A shekara ta alif 1970, Ussaini (Barde) ya yanke shawarar yin aikin hajji a shekara ta alif 1970, ya tafi aikin hajji ya bar wa dansa Yerima Ibrahim Ussaini Barde sarauta bayan ya koma gida ya ki karbar mulkinsa daga Yerima, a shekara ta alif 1970, Yerima Ibrahim ya zama sarkin Gubana. Sarki Barde ya rasu a shekarar ta alif 1996, ya yi shekara dari da biyar 105 da shekara arba'in 40 a matsayin sarki, kafin ya rasu ya bar ‘ya’ya 14 mata 6 da maza 8. Ya zuwa yanzu sarki Ibrahim Ussaini Barde shine sarkin Gubana yana da shekaru 96 a duniya, dansa Yerima idriss Ibrahim Barde ne yake wakilce shi a masarauta domin ya riga ya tsufa, Yerima ya fara gudanar da sarautar a shekarar dubu biyu da goma shabiyar 2015 zuwa yau.[2] akwai asibti a kauyen.[3]


Gubana ƙauyen ne da ke da mashahuri sosai waɗanda suka dace da noman dawa da wake.

Gubana tana da ilimi na Musulunci da na zamani suna yin karatun Islama a cikin nau'in gargajiya da ake kira Tsangaya. Kuma yawanci ana amfani da su (warash), a ilimin zamani suna da ilimin firamare wanda ya yi sama da shekaru 35 a ƙauyen.

Duk Gubana musulmi ne kuma kashi 85% na warash ne, yayinda sauran suke amfani da sunni. Masana'antu a farkon Gubana suna da sana'ar gargajiya kamar samar da farcen gatari wasu kuma aski na gargajiya, da kiwon dabbobi.

Gubana yana da iyaka da ƙauyuka a yammacin Maiwala, gabas Gubanan dutse, arewa kuma shine Ngubdo.

  1. http://www.maplandia.com/nigeria/yobe/fune/gurbana/gurbana-google-earth.html
  2. https://dailytrust.com/tags/idi-barde-guban[permanent dead link]
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-16. Retrieved 2022-01-16.