Jump to content

Ƴan sakai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ƴan sakai

Ƴan-Sakai ƙungiyoyin jami'an tsaro ne na sa kai a Najeriya musamman a yankunan arewa. An ƙirƙiro su ne saboda matsalolin tsaro da yankunan ke fuskanta tun 2010. Yan-Sakai a baya ana kiransu da Ƴan-Banga.

Zargi da Suka

[gyara sashe | gyara masomin]

Da yawa daga cikin ƴan-Sakai suna aikata laifuka daban-daban, kamar kashe mutanen da basuji-basu-gani ba, da wawashe dukiyoyi, da sauran ayyukan ta’addanci. Wannan yasa daya daga cikin ƴan bindiga suna shiga ƙauyuka, inda suke harbin kan-mai-uwa-da-wabi suna zairgin cewa duk ƴan banga ne na yankin, sannan kuma suna kwashe dabbobi da duk wani abu mai daraja suna masu ikirarin ganima suka samu.[1] Kasancewar waɗannan ayyukan da da basu dace ba da ƴan sakai sukeyi ya haifar da damuwa tare da sanya shakku a cikin aikin su game da fa'ida da amincin Yan-Sakai gaba daya. Saboda haka ne ma wasu daga cikin manyan mutane har da Malamai suka fara kira ga irin waɗannan ƙungiyoyin sakan da su rinƙa tantance mambobin su, kuma su tsaftace aikin su ta wannan hanyar ne zasu samu taimakon Allah da nasara babba a aikin su. Idan suka kama wanda ake zargi da aikata ta'addanci suyi bincike idan binciken su ya tabbatar masu da abinda suke zargin gaskiya ne sai su hukunta shi daidai da laifin yake aikatawa.

  1. Wan (26 July 2024). "violence activities".