Jump to content

2019 zaben gwamnan jihar Bauchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdeveniment2019 zaben gwamnan jihar Bauchi
Iri gubernatorial election (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Jihar Bauchi

An gudanar da zaɓen gwamnan Bauchi na 2019 a ranar 9 ga Maris, 2019 kuma aka kammala ranar 25 ga Maris 2019. Gwamna mai ci Abubakar Muhammad ya sha kaye a hannun jam'iyyar PDP Bala Muhammed a zaɓen gwamnan jihar Bauch na 2019.[1] Mista Bala Mohammed, tsohon ministan babban birnin tarayya, ya samu kuri’u 515,113 inda ya kayar da gwamna mai ci Abubakar Muhammad wanda ya samu kuri’u 500,625.[1][2]

An yi wa mutane 2,462,803 rajista a jihar. Yayin da jimillar masu jefa ƙuri'a 1,143,019 aka amince da su. An kididdige adadin 1,111,406 a matsayin sahihiyar kuri'u yayin da aka soke kuri'u 22,566.[2] Bala Muhammad ya samu nasarar lashe zaɓen ne a ƙarƙashin Muhamaad Kyari da kuri'u 515,113 akan gwamna mai ci Muhammad Abubakar wanda ya samu kuri'u 500,625. [2] Alkaluma sun nuna cewa Bala ne ya fara kayar da gwamnati mai ci tun bayan dawowar dimokradiyya a 1999.[3] Nan take abokin hamayyar Muhammad Abubakar da ya sha kaye ya karɓi shan kaye tare da taya Bala murna tare da yi masa fatan Alheri. [3]

An bayyana cewa kusan jam’iyyu 32 da Ƴan takararsu 20 ne suka haɗa kai da jam’iyyar Peoples Democratic Party kuma Bala Muhammad ya samu goyon bayan tsige Gwamna mai ci Muhammad Abubakar.[4] Wadannan jam’iyyun sun haɗa da da sauransu; United Progressive Party (UPP), Green Party of Nigeria (GPN), Change advocacy Party (CPP), All Peoples Movement (APM), All Blending Party (ABP), People's Democratic Party (PDP), Action Joint Alliance (AJA), Advance Peoples Democratic Alliance (APDA), Grassroots Development Party of Nigeria (GDPN) da Accord Party (AC).[5]

'Yan takara

[gyara sashe | gyara masomin]

Ga wasu daga cikin manyan ƴan takara bisa ga jam’iyyunsu.[6]

s/n Suna Jam'iyya matsayi
1. Abubakar Muhammad APC Gwamna
2. Bala Muhammad PDP Gwamna
3. Mohammed Ali Pate[7] PRP Gwamna
4. Ambasada Shu'aibu Ahmed Adamu NNPP Gwamna
  1. 1.0 1.1 Ugbodaga, Kazeem (2019-03-24). "PDP's Mohammed wins Bauchi governorship supplementary election". P.M. News (in Turanci). Retrieved 2021-03-30.
  2. 2.0 2.1 2.2 "INEC declares PDP's Bala Mohammed winner of Bauchi governorship election" (in Turanci). 2019-03-26. Retrieved 2021-03-30.
  3. 3.0 3.1 "INEC Declares PDP's Muhammed Winner of Bauchi Governorship Poll". THISDAYLIVE (in Turanci). 2019-03-26. Retrieved 2022-02-05.
  4. "PDP's Bala Mohammed Wins Bauchi Governorship Election". Channels Television. Retrieved 2022-02-05.
  5. "32 political parties, 20 gov candidates join forces with PDP against Bauchi gov". Punch Newspapers (in Turanci). 2019-03-05. Retrieved 2022-02-05.
  6. "2019: Abubakar, Pate, Bala Mohammed, 22 others make INEC list for Bauchi governorship". Daily Trust (in Turanci). 2018-11-10. Retrieved 2022-02-05.
  7. "Bauchi 2019: PRP candidate, Pate pledges new dawn for state". Vanguard News (in Turanci). 2018-12-03. Retrieved 2022-02-05.