Jump to content

Abba Ahimeir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abba Ahimeir (Ibraniyawa; 2 ga watan Nuwamba shekara ta 1897 zuw 6 ga watan Yuni shekara ta 1962) babban ɗan jaridar ne na Yahudawa y

kuma ya kasance ɗan tarihi, kuma mai fafutukar kan har kokin siyasa. Daya daga cikin masu ra'ayi na Revisionist Zionism, shi ne wanda ya kafa ƙungiyar Revisionist Maximalist na Zionist Revisionist Movement (ZRM) da kuma ɓoye Brit HaBirionim . Colin Shindler ya yi jayayya cewa ya kamata a raba taken 'Father of the Revolt ' daidai tsakanin Ze'ev Jabotinsky da Ahimeir . [1]

Tarihin rayuwar shi

[gyara sashe | gyara masomin]

Abba Shaul Gaisinovich An haife shi ne a Dolgoe, ƙauyen da ke kusa da Babruysk a Daular Rasha ( a Belarus). Daga shekara ta 1912 zuwa shekara t 1914, ya halarci makarantar sakandare ta Herzliya Gymnasium a Tel Aviv . Yayinda yake tare da iyalinsa a Babruysk don hutun bazara a shekara ta 1914, Yaƙin Duniya ya ɓarke kuma an tilasta masa kammala karatunsa a kasar Rasha. A shekara ta 1917, ya shiga taron Zionist na kasar Rasha a Petrograd kuma ya sami horo na noma a matsayin wani ɓangare na ƙungiyar HeHalutz ta Joseph Trumpeldor a Batum, Caucasus don shirya shi dan rayuwa a matsayin majagaba a Ƙasar Isra'ila. A shekara ta 1920, ya bar kasar Rasha kuma ya canza sunansa daga Gaisinovich ya mai da sunan shi Ahimeir saboda ɗan'uwan sa Meir dan ya rika tunawa da shi Meir shine dan uwan shi da ya mutu a yaƙi a shekarar yana yaƙi da 'yan Poland a lokacin kisan gilla.[2]

  1. Kaplan, Eran. The Jewish Radical Right. University of Wisconsin Press, 2005. p15
  2. Dr. Aba Ahimeir: The man who turned the tide Beit Aba