Abbas Umar Masanawa
Abbas Umar Masanawa (An haife shi a ranar 7 ga watan Agusta, shekarar alif 1969) kuma ya fito daga jihar Katsina. Ya yi karatun Noma a fannin tattalin arziƙi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar ta alif.1992.[1] Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Abbas Umar Masanawa a matsayin Manajan Daraktan Kamfanin Buga kuɗi da Haƙo Ma’adanai na Najeriya. Hakan ya biyo bayan shawarar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya bayar a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan Agusta 28, ga shugaban ƙasar, inda aka amince da shi.[2]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Abbas Umar Masanawa Ranar 7 ga watan Agustan 1969, a cikin tsohuwar birnin Katsina a Unguwar Masanawa. Ya fara karatun firamare ne a makarantar firamare ta Sararin Kuka, daga nan kuma ya tafi makarantar jeka ka dawo ta Ƙofar ƴan ɗaka, daga nan kuma ya tafi Kwalejin Barewa Zariya inda ya yi karatun Sakandare. Masanawa ya kammala karatunsa na digiri a babbar jami'ar Ahmadu Bello Zaria da digirin digirgir a fannin tattalin arziƙin noma sannan kuma ya yi karatun MBA a jami'ar Same kafin ya wuce jami'ar Havard.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Masanawa shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Buga kuɗi da Haƙo Ma’adanai na Najeriya @NSPMC, wanda ya shafe sama da shekaru ashirin (20) yana gogewa a ɓangarori daban-daban, ya kasance Mataimakin Babban Manaja na Bankin Zenith Plc, mai ba Gwamnan Babban Bankin Najeriya shawara na musamman sannan kuma ya naɗa shi a matsayin Babban Daraktan Kudi da Dabaru a Kamfanin Buga kuɗi da Ma'adinai na tsaron Najeriya.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-01-03. Retrieved 2023-01-14.
- ↑ https://theeagleonline.com.ng/tag/abbas-umar-masanawa/
- ↑ https://www.nairaland.com/7123314/abbas-umar-masanawa-joins-katsina