Abdessalem Mansour
Abdessalem Mansour | |||
---|---|---|---|
29 ga Augusta, 2008 - 17 ga Janairu, 2011 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Sousse (en) , 19 Nuwamba, 1949 (74 shekaru) | ||
ƙasa |
French protectorate of Tunisia (en) Tunisiya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Tunis University (en) University of Minnesota (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da injiniya |
Abdessalem Mansour (an haife shi ranar 19 ga watan Nuwamba, 1949) ɗan siyasan Tunusiya ne. Ya kasance Ministan Aikin Gona a lokacin tsohon shugaban kasar mai suna Zine El Abidine Ben Ali .
Haihuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mansour a Sousse, Tunisia . [1] Ya kammala karatunsa a jami’ar Tunis a shekarar 1971, sannan ya samu digiri na biyu a fannin ilimin aikin gona daga jami’ar Minnesota a shekarar 1974.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Daga shekarar 1974 zuwa 1980, ya yi aiki a Ma’aikatar Noma ta Tunusiya. Ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga wani kamfanin kasar Kuwaiti daga shekarata 1980 zuwa 1981. [1] Daga 1981 zuwa 1999, ya yi aiki da bankin Stusid . A watan Agustan shekarar 2008, an nada shi a matsayin Ministan Aikin Gona da Albarkatun Ruwa, har sai da aka sauke shi bayan abin da ya biyo bayan zanga-zangar Tunusiya ta 2010-2011 .