Jump to content

Abdullahi Garba Aminchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdullahi Garba Aminchi
Rayuwa
Haihuwa 1954 (69/70 shekaru)
Sana'a

Abdullahi Garba Aminchi (an haife shi a ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 1954) a Funtua LGA, Jihar Katsina) ya kasance mataimakin gwamnan gwamnatin NRC ta Najeriya karkashin jagorancin Alhaji Saidu Barda daga 1992 zuwa 1993. Ya kasance mataimakin Gwamna Umaru Musa Yar'Adua a shekara ta 2003. Ya rike mukamin Jakadan Saudi Arabia da Oman a lokacin mulkin shugaban kasa na Umaru Musa Yar'adua daga shekara ta 2007.

Abdullahi Garba ya bar fagen injiniya don shiga siyasa. Ya fara ne a matsayin sakataren jam'iyya, sannan kuma wakilin shugaban sannan daga baya mataimakin gwamna ga Saidu Barda a 1992 kuma a 2003 ga Umaru Musa Yar'Adua . [1] Bayan gwamnan Umaru Musa Yar'Adua ya tsaya takarar shugaban kasa kuma ya lashe a 2007, an sanya Garba jakadan Najeriya a Saudi Arabia da Oman.[2]

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Rashin karbar gyara ya sa na fita daga PDP – Garba Aminchi". Aminiya (in Turanci). 2014-10-09. Retrieved 2022-06-16.
  2. "How Yar'adua short-changed Southern Katsina". Sahara Reporters. 2009-06-29. Retrieved 2022-06-16.