Jump to content

Abdullahi Kanu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdullahi Kanu
Kanu
Wikimedia disambiguation page (en) Fassara

Abdullahi Kanu (An haifeshi a ranar 19 ga watan Oktoba 1999) an haifeshi a jihar Katsina, Najeriya. ya kasance ɗan kwallon ƙafa wanda yake taka leda a kungiyar K. Soro United.

Abdullahi Kanu ya kasance dan wasan gaba wanda ke buga lamba 11. Sai dai dan wasan yana buga lamba 7 da kuma lamba 9.

Rayuwar Baya

[gyara sashe | gyara masomin]

Abdullahi Kanu ya fara buga kwallo a kungiyar J. Brazilian tun yana dan shekara 12 a shekarar 2012, inda ya shafe shekaru 4 yana taka leda a kungiyar ta J. Brazilian inda ya lashe kofuna 8 a kungiyar. ya buga wasanni 133 tare da kungiyar, ya zura kwallaye 117 ya taimaka anci kwallaye 71, a jumullar gudummawa kuma ya kama 188. ya kasance ɗan wasan da yafi kowa zura kwallaye a tarihin ƙungiyar.

Dan wasan ya canza sheƙa zuwa kungiyar Royal F. C shekarar 2016 inda ya zama kwararren dan kwallo a tarihin rayuwar shi. [1]

Aikin Kwararrun Ƙungiyoyi

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2016 ya koma ƙungiyar Royal F. C a ƙarkashin mai horaswa Abey inda ya buga wasanshi na farko a Ƙungiyar da Wigan F. C. Royal F. C tayi nasara a wasan daci 3-1, yayin da Abdullahi Kanu ya jefa kwallo ɗaya a raga.

Ya shafe shekara 1 a kungiyar Royal F. C inda ya buga wasanni 24, ya zura kwallaye 20 ya taimaka an zura kwallaye 11. dan wasan ya kasance ɗan wasan da yafi kowa zura kwallo a kungiyar ta Royal F. C a shekarar. [2]

Shooting Star

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2017 dan wasan ya kulla yarjejeniya da kungiyar Shooting star da kwantiragin shekaru 2 a ƙarƙashin jagorancin mai horaswa Hamisu Kaftin.

Ya buga wasan farko da kungiyar 11 shooting inda sukayi rashin nasara daci 2-1 a wasan, sai dai dan wasan ya zura kwallon sa ta farko a wasan.[3]

Ya shafe tsawon shekaru 2 a Ƙungiyar (2017-2019) a Ƙungiyar ta Shooting Star, ya buga wasanni 30, ya zura kwallaye 19, ya taimaka an zura 13.

Kkt Strikers

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2019 ya zama ɗan wasan KKT. sai dai dan wasan ya fuskanci matsaloli na rashin buga wasanni a kungiyar inda ya buga wasanni 4 kacal yaci kwallo ɗaya tare da kungiyar a ƙarƙashin mai horaswa Dashin.

Dawowa Shooting Star

[gyara sashe | gyara masomin]

Abdullahi Kanu ya sake dawowa tsohuwar ƙungiyar Shooting Star a shekarar alif 2020 inda ya shafe tsawon shekara 1 a kungiyar, ya buga wasanni 24 yaci kwallaye 18 ya taimaka aka zura kwallaye 8 a raga. dan wasan ya shiga cikin jerin manyan yan wasa na tarihin ƙungiyar inda ya kawo nasarori a kungiyar.

Ya raba gari da kungiyar Shooting Star a shekarar 2021 inda ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Gawo Professional.[4]

Gawo Professional

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2021 ya kulla yarjejeniya da ƙungiyar Gawo Professional inda ya shafe shekaru 3 a kungiyar. dan wasan ya buga wasanni 54 a kungiyar inda ya zura kwallaye 40 ya taimaka akaci kwallaye 18.[5]

A shekarar 2023 dan wasan ya lashe kyautar zama gwarzon dan wasa a kungiyar Gawo Professional.[6]

Gasar Super lig 2023

[gyara sashe | gyara masomin]

Abdullahi Kanu ya taka rawar gani a gasar Super lig na shekarar 2023, inda ya zama dan kwallon da yafi kowa jefa kwallo a gasar da kwallaye 6 sai Abu Awara dake bimashi da kwallaye 5.

Ya kai matakin kusa da na karshe tare da kungiyar Gawo Professional inda sukayi rashin nasara a wasan da kungiyar Durɓi Strikers daci 2-1 inda dan wasan shine yaci ɗayar da sukaci.[6]

A shekara ta 2023 ya kulla yarjejeniya da kungiyar Monaco Atc inda ya shafe watanni 4 kacal tare da kungiyar inda ya buga wasanni 18 a Ƙungiyar. ya zura kwallaye 14 a Ƙungiyar.[7]

11 Shooting

[gyara sashe | gyara masomin]

A karshen shekarar 2023 dan wasan ya koma ƙungiyar 11 shooting inda ya shafe tsawon watanni 3 tare da kungiyar inda ya zura kwallaye 10 a cikin wasanni 21 da ya buga tare da ƙungiyar.

Bayan raba gari da kungiyar 11 Shooting, dan wasan ya kulla yarjejeniya d kungiyar Kangiwa United a ranar 6 ga watan Mayu, sai dai ya shafe watanni 2 kacal a kungiyar inda ya buga wasanni 10 yaci kwallaye 8.[8]

Dan wasan ya raba gari da ƙungiyar a ranar 18 ga watan Yuni 2024.

A cikin watan Agusta 2024 dan wasan ya kulla yarjejeniya da kungiyar K. Soro inda ya buga wasanni 9 yaci kwallaye 5 daga Agusta zuwa yanzu. ya samu lambar yabo daga magoya bayan kungiyar inda ya zura kwallo a wasan hamayya da suka fafata da kungiyar Kangiwa, inda suka samu nasara daci 1-0.[9]

  1. Abdullahi Kanu Joins Royal F.C." Royal F.C. Official Website, 2016.
  2. Abdullahi Kanu Joins Royal F.C." Royal F.C. Official Website, 2016.
  3. "Shooting Star Signs Abdullahi Kanu." Shooting Star F.C. Official Website, 2017
  4. Abdullahi Kanu Returns to Shooting Star." Shooting Star F.C. Official Website, 2020.
  5. "Gawo Professional Signs Abdullahi Kanu." Gawo Professional F.C. Official Website, 2021.
  6. 6.0 6.1 Abdullahi Kanu Wins Best Player Award." Gawo Professional F.C. Official Website, 2023
  7. Joins Monaco Atc." Monaco Atc Official Website, 2024.
  8. "Kangiwa United Signs Abdullahi Kanu." Kangiwa United F.C. Official Website, 2024.
  9. "Abdullahi Kanu Joins K. Soro." K. Soro United F.C. Official Website, 2024.