Abiodun Alabi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abiodun Alabi
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da police commissioner (en) Fassara

Abiodun Sylvester Alabi (an haife shi 31 ga watan Disamba a shekarar 1964 a Ilawe Ekiti) kwamishinan ƴan sandan Najeriya ne. Shi ne kwamishinan ƴan sanda na rundunar ƴan sandan jihar Legas, mai muƙamin mataimakin babban sufeton ƴan sanda.

Ilimi da Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Alabi ya yi digirinsa na farko a fannin ilimin zamantakewa a Jami’ar Legas a shekarar 1986, sannan ya yi digiri na biyu a irin wannan fanni a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife a 1989. Ya shiga aikin ƴan sandan Najeriya a watan Maris 1990 a matsayin jami’in kadet.

A watan Janairun 2022, Alabi ya maye gurbin Hakeem Odumosu a matsayin kwamishinan ƴan sandan jihar Legas. Ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan ƴan sandan jihar Bauchi, da kuma kwamishinan ƴan sanda mai kula da rejista na manyan laifuka, sashin binciken manyan laifuka na rundunar Annex, Alagbon a Legas. Ya kasance tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sandan Taraba da jihar Ekiti, kuma tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda na rundunar ƴan sanda ta wayar salula. A shekarar 2001, ya kuma yi aiki da Ofishin Jakadancin Majalisar Ɗinkin Duniya a Kosovo (UNMIK).

Alabi mamba ne a Kwalejin Tsaro ta Najeriya kuma memba ne a Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya. Shi ma memba ne a ƙungiyar shugabannin ƴan sanda ta duniya.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]