Jump to content

Adam Abdullahi Adam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Adam Abdullahi Adam wanda a kafi sani da (Daddy hikima ko kuma Abale) jarumi ne a masana'antar shirya fina-finan Hausa (kannywood) yana daga cikin jarumai da yanzu tauraran su ke haskawa a masana'antar ya fito a jerin shirye-shirye masu yawa wanda hakan yabashi farin jini a arewacin Najeriya Shirin da yafi ɗaukaka daga cikin shirye-shiryen daya fito sune kamar haka ana masa inkiya da Abale,sanda,ojo Sanda, A Duniya da dai sauransu.[1]

Rayuwar farko da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Daddy Hikima, An haifeshi a ranar 16 ga watan maris shekarar 1991 a jihar kano ta Najeriya, wanda a yanzu ya nada shekaru 32 a duniya. Ya fara karatu duk a jihar Kano, inda yayi firamarinsa, sannan ya hurce makarantar sakandiri duk a Kano, daga nan ne ya tafi makarantar koyon jinya da unguwarzoma. Daddy hikima ya shiga harkan fina-finan hausa a shekarar 2020 inda ya shahara bayan ya fito a wani shiri mai dogon zango wanda ake kira da A duniya wanda tijjani asase ya shirya.

Wasu daga cikin fina-finansa

[gyara sashe | gyara masomin]
  • A duniya
  • Sanda
  • Haram
  • Uku sau Uku
  • Labarina
  • Asin da Asin
  • Farin wata
  • Yan zamani
  • Na ladidi
  • Makaryata

yayi aure a 27 ga watan junairun shekarar 2023 a karamar hukumar kumbotso.[2]

  1. "Daga Bakin Mai Ita tare da Daddy Hikima". BBC Hausa.Com. 31 August 2023. Retrieved 7 October 2023.
  2. Khalid, Aisha (24 January 2023). "Jarumi Abale Zai Angwance, Katin Auren da Hoton Kyakyawar Amaryarsa Sun Fito". legit.hausa.ng. Retrieved 7 October 2023.