Agnes Mukabaranga

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Agnes Mukabaranga
Member of the Pan-African Parliament (en) Fassara


Member of the Senate of Rwanda (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Ruwanda, 20 century
ƙasa Ruwanda
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Agnes Mukabaranga

Agnes Mukabaranga 'yar siyasa ce ta ƙasar Rwanda . [1] Mukabaranga memba ce ta Jam'iyyar Demokradiyyar Kirista (PDC) kuma ’yar majalisa ce a Majalisar Dokokin Pan-Afirka kuma tsohon memba na Majalisar Dokoki da Majalisar Dattijan Rwanda . [1] Ta kasance lauya ce a sana’ance.[2]

Ayyukan siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An nada Mukabaranga a matsayin memba ta farko ta Majalisar Dokoki ta Kasa ta rikon kwarya, wanda aka kafa bayan Kisan kare dangi na Rwanda na 1994, kuma hakan sun dogara ne akan Yarjejeniyar Arusha da aka amince da ita a shekarar da ta gabata. A shekara ta 2003, an amince da sabon kundin tsarin mulki na dindindin a kasar na raba gardama, wanda ya kafa jam'iyyun jam'iyya da yawa tare da majalisa mai ‘yan majalisu biyu wanda ta kunshi majalisar dattijai da majalisar wakilai. An nada Mukabaranga a sabuwar majalisar dattijai bayan zaben Paul Kagame a matsayin shugaban farko a karkashin sabon kundin tsarin mulki. [1] [3] Ta zamo ɗaya daga cikin mata 39 da aka zaba ko aka nada a majalisa a wannan shekarar, idan aka kwatanta da maza 41.[2] Ta yi alkawarin yin gwagwarmaya don adalci da sulhu a cikin ƙasar bayan kisan kare dangi, ta jaddada rawar da mata ke takawa a cikin tsari, tana cewa "Mata sun fi son suyi sulhu, sun fi son zaman lafiya kuma sun fi sasantawa".[5][2]

A shekara ta 2013, bayan da ta bar majalisar dattijai, an zabi Mukabaranga na tsawon watanni shida a matsayin mai magana da yawun kungiyar Bada shawarwari ra Kasa akan Jam’iyyun Siyasa, rawar da ta taka tare da ma'aikaciyar jinya da sabon dan siyasa, Sylvie Mpongera na Jam'iyyar Socialist Party (PSR).

Rayuwar ta[gyara sashe | gyara masomin]

Agnes Mukabaranga ta rasa 'yan uwanta a yayin yakin basadan Rwanda, kuma ta kasance mahaifiyar yara hudu ce.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Parliament of Rwanda. "MUKABARANGA Agnés". Archived from the original on 23 October 2007. Retrieved 30 October 2016.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 Wuerth, Hans M. (20 April 2004). "The people of Rwanda deserve our support". Archived from the original on 28 June 2018. Retrieved 28 October 2016. Cite error: Invalid <ref> tag; name "HansWuerth" defined multiple times with different content
  3. Nunley, Albert C. "Elections in Rwanda". African Elections Database. Retrieved 9 February 2013.